Jerin sunayen kwararru 14 da Buhari ya nada don yin garambawul ga tsaron Najeriya

Jerin sunayen kwararru 14 da Buhari ya nada don yin garambawul ga tsaron Najeriya

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta rantsar da wasu kwararru su goma sha hudu data daura ma alhakin sabuntawa tare da inganta harkar tsaro da kuma tsara aikin yan doka a Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnati ta zabo wadannan kwararru ne bayan kimanin mako guda da shugaba Buhari ya umarci babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohammed Adamu ya fara aiwatar da tsarin yan doka a duk fadin Najeriya.

KU KARANTA: Abin kunya: An kaure da dambe a zauren majalisa, an karairaya sandan iko

Jerin sunayen kwararru 14 da Buhari ya nada don yin garambawul ga tsaron Najeriya
Majalisar tsaro
Asali: Facebook

Sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha ne ya jagorancin rantsar da kwamitin a ofishinsa dake fadar gwamnatin tarayya, Aso Rock Villa, inda yace shugaban kasa ya bukaci daliban cibiyar horas da manyan jami’an gwamnati dake Kuru dasu gudanar da bincie akan matsalar tsaro a Najeriya.

Mustapha ya bayyana cewa gwamnati na bukatar rahoton kwamitin cikin watanni biyu kacal, don haka yayi kira a garesu dasu zage damtse, su dage wajen gudanar da wannan aiki, tare da baiwa gwamnati shawarwari masu amfani.

Shugaban kwamitin itace Amina Shamaki, Mrs. Beatrice Jeddy-Agb, Mrs. Odunbanjo Adebisi, Sanusi Galadim, Brig-Gen J. O. Ochai and Commodore J. N. Mamman, Air Cdre A. H. Bakari, AIG David O. Folawiyo, Jimat Bakare, CP Olayinka Balogun, Dakta. E.O. Adeoye, Dakta. Joseph Ochogwu, Farfesa Sani Abubakar Lugga, Dakta Nasirudeen Usman, da Tukur Yahaya sakataren kwamitin.

Sai dai Mustapha ya bayyan wasu matsaloli dake kawo tasgaro ga tsaro a Najeriya da suka hada da rashin aiwatar da tsare tsaren gwamnati yadda ya kamata, rashin sa ido a aikin tsaro, rashin amfanin da kimiyya da fasaha wajen tsaro, rashin samuni isassun kudade, rashin aminta da jami’an tsaro daga yan Najeriya da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel