Alkalai masu shari’a su na samun matsalar albashi da alawus - Inji Sani

Alkalai masu shari’a su na samun matsalar albashi da alawus - Inji Sani

Mun ji cewa Sanata Shehu Sani ya fito yayi magana a game da sha’anin albashin Malaman shari’a a Najeriya. Fitaccen ‘Dan Majalisar ya koka da halin da Alkalai su ke ciki na rashin albashi da kuma alawus din su na aiki.

Shehu Sani wanda ke wakiltar Yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan kasar ya fito ya bayyana cewa an yi shekara guda cur kenan Alkalai masu shari’a ba ya motsawa a Najeriya. Babban Sanatan yace hakan bai dace ba.

Bayan batun albashi, Sanatan na jam’iyyar adawa ta PRP, ya bayyana cewa Alkalan kasar ba su samun alawus din su yadda ya kamata a cikin ‘yan shekaraun nan. Shehu Sani, yace akwai hadari wajen rashin ba Alkalai hakkinsu.

Sanatan yake cewa babu yadda za ayi tunani Alkalai za su yi adalci a shari’a muddin ba su karbar hakkinsu daga hannun gwamnati. Sani yana tsoro rashin kudin Alkalan ya sa su rika karbar cin hanci wajen saida gaskiya.

KU KARANTA: Yadda Sojoji su ka kashe mutane a lokacin zaben 2019 - Gwamnan Ribas

Alkalai masu shari’a su na samun matsalar albashi da alawus - Inji Sani
Sanata Shehu Sani a lokacin yana jawabi a cikin zauren Majalisa
Source: Depositphotos

‘Dan majalisar yake cewa tun farko dai Alkalan ba su da wani albashin kirki sannan kuma bugu-da-kari, ana samun matsala wajen biyan su wannan kudi, Sanatan yace akwai bukatar ace Alkalai masu shari’a su na cikin masu cabawa.

An kuma ji Sanatan yana bayani a kaikace yana caccakar gwamnan Kaduna bayan yayi jawabi a kan yadda za a daina siyasar uban-gida. Sanatan ko da bai kama suna ba, ya nuna cewa gwamnan da bazar Uban gidan sa yake rawa a yau.

Wannan fitaccen Sanata yayi wannan bayani ne a shafin sa na Tuwita a Ranar Litinin 6 ga Watan nan. Sanatan wanda ya bar APC a bara ya saba fitowa kafofin sadarwa yayi magana kan batun kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel