Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An yiwa Sarki yankan rago a jihar Sokoto
- Wasu 'yan bindiga sun yiwa wani mai gari yankan rago da tsakar yamma a jihar sokoto
- 'Yan bindigar sun iske mai garin har gida suka yanka shi bayan sun gama harbin kan mai uwa da wabi a cikin garin
Da yammacin jiya Talata ne wasu 'yan bindiga suka kai hari karamar hukumar Mulkin (Gudu) dake cikin jihar Sokoto, inda suka yiwa Sarkin garin yankan rago, bayan sun gama harbin kan mai uwa da wabi a cikin garin.
Wani mutumi mai suna Babangida Sada shi ne ya sanya labari a shafinsa na Facebook, mutumin ya bayyana cewa 'yan bindigar sun yiwa garin tsinke jiya Talata da yamma, inda suka dinga harbe-harbe ba kakkautawa a cikin garin, bayan sun kammala cin zarafin mutanen garin, sai suka wuce gidan mai gari, inda suka kama shi suka yi masa yankan rago.
Matsalar tsaro dai taki ci taki cinyewa a Najeriya musamman ma a yankin arewa da ake ganin maimakon matsalar ta dinga samun koma baya, kullum sai kara cigaba ta ke yi.
A makon da ya gabata ne aka sace Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar, wanda 'yan bindiga suka je har gidanshi da ke garin Daura da Magariba suka yi awon gaba dashi.
KU KARAANTA: Tirkashi: Sarkin Katsina ya bai wa Ministoci sako su kaiwa shugaba Buhari
Hakimin wanda aka bayyana shi a matsayin siriki ga babban dogarin shugaban kasa Muhammadu Buhari, har yanzu babu amo babu labarin ainahin inda yake.
Hakazalika a jiya ne kuma sarkin Katsina Mai Girma Abdulmumini Kabir Usman ya bukaci ministan noma, Audu Ogbeh da ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa manoma da makiyaya na jihar Katsina, sun bar gonakin su da dabbobin su saboda tsoron masu garkuwa da mutane. Inda ya bukaci shugaban kasar ya fara samar da tsaro a yankin kafin mutane su samu damar gabatar da noman da ya ke so.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng