UCL: Liverpool ta ga bayan Barcelona a wasan zagayen kusa da na karshe

UCL: Liverpool ta ga bayan Barcelona a wasan zagayen kusa da na karshe

Liverpool, kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila, ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta kasar Spain, Barcelona da ci 4 da nema (0) a wasan zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

An buga wasa na biyu tsakanin Liverpool da Barcelon a filin wasa na Anfiled dake garin Liverpool a kasar Ingila a ranar Talata.

A wasa na farko da aka buga ranar 1 ga watan Mayu, 2019, a kasar Spain, kungiyar Barcelon ta samu nasara a kan kungiyar Liverpool da ci uku da nema (0).

Tuni masu kallo da masu hasashen wasan kwallon kafa suka bayyana cewar zai yi matukar wuya kungiyar Liverpoool ta kai ga zagaye na karshe bayan ta kwashi kashinta a hannu a gidan Barcelona. Sai kungiyar Liverpool ta saka a kallo kwallo hudu a ragar kungiyar Barcelona kuma ba a saka ko daya a ragar ta ba, kafin ta samu damar tsallaka wa zuwa zagaye na karshe.

Mintuna 7 da fara wasa a gidan Liverpool, dan wasan gaba na kungiyar, Origi, ya zira kwallon farko a ragar Barcelona. Kwallon ta makale har zuwa hutun rabin lokaci.

UCL: Liverpool ta ga bayan Barcelona a wasan zagayen kusa da na karshe
Dan wasan Liverpool, Origi, ya zira kwallo ta biyu a ragar Barcelona
Asali: Getty Images

Jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne dan wasan tsakiya na Liverpool, Wijnaldum, ya saka kwallo ta biyu a ragar Barcelona, kafin daga bisani ya kara zira kwallo ta uku bayan 'yan mintuna kadan.

Origi, dan wasan Liverpool da ya ci kwallo ta farko, ne ya kara zira kwallo a ragar Barcelona a wata kwana ta shammace da kungiyar Liverpool ta dauka.

DUBA WANNAN: Ta tabbata, Farfesa Tijjani Bande ya zama sabon shugaban majalisar wakilan UN

Liverpool ta buga wasan ba tare da manyan 'yan wasanta guda uku da suka samu rauni ba. 'Yan wasan sune: fitaccen dan wasan gaba; Mohammed Sala, da takwaransa da suke taka leda tare ;Firmino, sai kuma dan wasan tsakiya; Keita.

Nasarar da kungiyar Liverpool ta samu ta matukar bayar da mamaki, musamman ganin cewar kungiyar Barcelona da ta gagari kungiyoyi da dama suka lallasa da ci 4 da 0.

Yanzu haka Liverpool ta tsallaka zagaye na karshe na gasar UCL, inda zata jira wanda zai samu nasara a tsakanin kungiyar Ajax ta kasar Netherland da Tottenham ta kasar Ingila a wasa na biyu da zasu buga a ranar Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel