An kashe mutum 50, an raunta 30 bayan an kai hare-hare a Zamfara
‘Yan bindiga sun hallaka Bayin Alla da-dama a wasu hare-hare har 3 da aka kai a cikin Garuruwan jihar Zamfara a karshen makon jiya. Jaridar Punch ta rahoto adadin mutanen da aka kashe a jihar.
Akalla mutane 50 ne aka hallaka, bayan an ji wa wasu 31 rauni a cikin hare-haren da aka kai cikin Zamfara kwanan nan. Wasu ‘Yan bindiga dai sun hana mutanen yankin Dangurgu, kunkilai, da Birnin Magaji sakat a cikin kwanakin nan.
Hari 3 aka kai a cikin wadannan Garuruwa da ke cikin kananan hukumomin Maru, Gusau da kuma Birnin Magaji a karshen makon da ya gabata, Hakan na zuwa ne bayan jami’an tsaro sun yi azamar kawo karshen ta’adin da ake yi a jihar.
KU KARANTA: Abin da ya sa aka gaza kawo karshen matsalar satar mutane
Dakarun ‘yan sanda sun kaddamar da wani shiri na ‘Operation Puff Adder’ da ake sa rai zai kawo karshen kashe mutanen da ake yi a Garuruwan Zamfara da kewaye. Amma sai ga shi an kashe mutum 50 a Ranar Asabar da ta wuce.
Kamar yadda mu ka samu labari, wadannan ‘yan bindiga sun shiga Kauyen Kunkilai ne a Ranar 4 ga Watan Mayun nan inda su ka budawa wasu masu halartar bikin suna wuta. A nan-take aka kashe mutane 30, kuma aka raunata mutum 6.
A Ranar Juma’a kuma ‘Yan bindiga su ka kashe mutum 20 a Garin Magami da ke cikin Gusau, an kuma yi wa mutum 15 rauni a harin daga ciki har da sojoji. Jami’an tsaro sun tabbatar da aukuwar wannan hari bayan ‘yan bindigan sun tsere.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng