Jam'iyyu 75 sun amince da sakamakon zaben shugaban kasa na 2019

Jam'iyyu 75 sun amince da sakamakon zaben shugaban kasa na 2019

Kimanin jam'iyyun siyasa 75 a fadin Najeriya a ranar Litinin sun cimma matsaya tare da bayyana matakin su kan shugaban hukumar zabe ta kasa INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, biyo bayan gudanar babban zaben kasa na 2019.

Shugaban hukumar zabe; Farfesa Mahmoud Yakubu

Shugaban hukumar zabe; Farfesa Mahmoud Yakubu
Source: UGC

Jam'iyyun siyasa 75 a fadin Najeriya sun bayyana aminci tare da amanna akan kwazon shugaban hukumar INEC dangane da samun abun da su ka bayyana a matsayin ingatacciyar nasara yayin kammala zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a ranar 23 ga watan Fabrairu da kuma na gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, jam'iyyun sun yi itifakin cewa gudanar babban zaben kasa na bana ya yi daidai da cikar burikan mafi akasarin al'ummar Najeriya.

Shugabannin jam'iyyun sun cimma wannan matsaya a yayin wani zama na kwanaki biyu da suka aiwatar cikin babban birnin kasar nan na tarayya domin fayyace duk wata harkalla da ta gudana a yayin babban zabe na bana.

Sai dai jam'iyyun sun yi babbatu na bayyana yadda hukumomin tsaro musamman dakarun soji su ka haifar da duk wata tagarda da kuma cikas da aka fuskanta a yayin gudanar da zaben.

KARANTA KUMA: Ziyarar da na kai birnin Landan ba ta da alaka da nadin Ministocin Majalisa ta - Buhari

Domin kaucewa maimacin makamancin wannan abun ki, jam'iyyun sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan gaggauta sanya hannu cikin sabon kudiri na sauya salon zaben kasar nan.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon mataimakin shugaban kasar Sierra Leone, Alhaji Sam Sumana, ya halarci babban taron bisa jagorancin Farfesa Remi Aiyede da aka gudanar cikin babban dakin taron kasa da kasa na ICC da ke garin Abuja.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel