Buhari ya amince da nadin Bello Maitama a matsayin darekta a NRC

Buhari ya amince da nadin Bello Maitama a matsayin darekta a NRC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin tsohon ministan kasuwanci, Bello Maitama Yusuf, a matsayin daya cikin darektocin hukumar harkokin jiragen kasa ta Najeriya (NRC)

Yusuf, mai shekaru 72, ya taba yin gudun hijira domin guje wa dauri bayan gwamnatin mulkin soji ta shugaba Buhari ta zarge shi da cin hanci.

An nada Yusuf a matsayin ministan harkokin cikin gida a shekarar 1972 lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Shehu Shagari, kafin daga bisani a nada shi a matsayin ministan kasuwanci a shekarar 1982.

Yusuf da marigayi Umaru Dikko ne a sahun gaba a cikin jerin sunayen manyan gwamnatin Shagari da Buhari ya shiga nema ruwa a jallo domin daure su saboda samun su da laifin aikata cin hanci, lamarin da ya tilasta su yin gudun hijira su bar Najeriya.

Buhari ya amince da nadin Bello Maitama a matsayin darekta a NRC
Buhari ya amince da nadin Bello Maitama a matsayin darekta a NRC
Asali: Twitter

Auwal Sankara, mai taimakawa gwamnan jihar Jigawa a bangaren yada labarai a kafafen sadarwar zamani, ne ya tabbatar da nadin Yusuf a wani jawabi da ya fitar a shafinsa na dandalin sada zumunta (Facebook).

A wasikar da ke dauke da bawa Yusuf mukamin, kamar yadda majiyar mu ta gane wa idonta, an rubuta cewar: "bisa dogaro da sashe na 5 na kundin hukumar NRC mai lamba N129, LFN2004, da kuma kuma ikon da ministan sufuri ke da shi bisa dogaro da zabar ka da gwamnan jihar Jigawa ya yi, ina mai farincikin sanar da kai cewar an nada ka a matsayin daga cikin darektocin hukumar NRC".

DUBA WANNAN: Dawowar buhari: Fadar shugaban kasa ta gwasale 'yan adawa da kafafen yada labarai

Sankara ya kara da cewa nadin Yusuf ya biyo bayan irin gudunmawar da ya bayar wajen cigaban jam'iyyar APC a jihar Jigawa da Najeriya bakidaya.

Tun a ranar Alhamis ne ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya rantsar da Yusuf da ragowar darektocin da aka nada har ya bukaci da su yi amfani da gogewar su wajen bayar da gudunmawa a kokarin da gwamnati ke yi na inganta sufuri a jiragen kasa, kamar yadda jaridar 'The Guardian' ta rawaito

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel