Jonathan, Atiku da Saraki sun yi alhinin tunawa da mutuwar tsohon shugaban kasa 'Yar adu'a

Jonathan, Atiku da Saraki sun yi alhinin tunawa da mutuwar tsohon shugaban kasa 'Yar adu'a

Shekaru 9 da suka gabata a daidai rana irin ta yau, 5 ga watan Mayun 2010, tsohon shugaban kasar Najeriya Marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar Adu'a, ya riga mu gidan gaskiya bayan ya sha fama da tsawaitacciyar rashin lafiya.

Marigayi 'Yar Adu'a ya rasu ya bar ma dakin sa, Hajiya Turai 'Yar Adu'a da 'ya'ya tara da suka hadar da Mata biyar da kuma Maza hudu. An yi jana'izar sa a mahaifar sa ta jihar Katsina a ranar 6 ga watan Mayun 2010.

Al'ummar Najeriya da dama musamman a dandalan sada zumunta na ci ga da ta'aziyya tare da nuna alhinin mutuwar sa bayan shekaru tara da barin duniya. Jama'a da dama na tunawa da wasu ababen alheri da dasa a kasar nan yayin riko da akalar jagoranci.

Tsohon shugaban kasa, Marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar Adu'a
Tsohon shugaban kasa, Marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar Adu'a
Asali: UGC

Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan da ya ci gajiyar mulkin kasar nan a hannun Marigayi 'Yar Adu'a, ya tuna da ubangidan sa inda cikin wasu sakonni a shafin sa na sada zumunta ya kwarara yabo da jinjina a gare sa kan wasu muhimman da ya shimfida na gina kasa a zamanin sa.

Jonathan ya misalta Marigayi 'Yar Adu'a a matsayin jagora da ya fifita inganta ci gaba kasa sama da soyuwar zuciyar cikin managarcin tsarki ba tare da nuna banbanci na kabilanci ko kuma akida ta siyasa.

KARANTA KUMA: Dole na kammala aikin gadar Neja ta biyu a Kudu maso Gabas - Buhari

Kazalika tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ba a bar shi a baya ba wajen nuna alhinin Mutuwar marigayi tsohon gwamnan jihar Katsina. Ya yaba masa musamman a kan kasancewar sa jagora da ya azurta da jin kai da kuma kishin kasa.

Yayin rokon Ubangijin Talikai akan ya jikan sa tare da dawwamar da rahama a gare shi, shugaban Majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki tare da wakilin shiyyar Kaduna ta Tsakiya a majalisar, Sanata Shehu Sani, sun hikaito yadda Marigayi 'Yar Adu'a ya tsarkaka da rikon amana da kuma gaskiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel