Kasashe 10 da suke biyan albashi mafi karanci a 2019

Kasashe 10 da suke biyan albashi mafi karanci a 2019

Jerin kasashe a duniya da suke biyan albashi mafi karanci ga ma'aikatan su

Maganar da ake yi akan karin albashi domin jin dadin ma'aikata ba wai iya a Najeriya ba ne. Ma'aikata a fadin duniya kullum kokari suke suga sun samu kari a albashin da ake biyansu.

A cewar Nomad Capitalist, neman karin albashin ma'aikata ya samo asali ne a karni na 19, duk da dai masana a fannin tattalin arziki ba su yadda cewa karin albashin ya na ingantan tattalin arzikin kasa ba.

Kasashe 10 da suke biyan albashi mafi karanci a 2019

Kasashe 10 da suke biyan albashi mafi karanci a 2019
Source: Depositphotos

Abin mamaki ne, idan ku ka luracewa wasu kasashen da suke da kyakkyawan cigaban tattalin arziki amma har yanzu suna biyan ma'aikatansu mafi karancin albashi a duniya.

A cewar jaridar Nomad Capitalist, ta kawo muku jerin wasu kasashe 10 a duniya da suke biyan ma'aikatansu albashi mafi karanci a wata:

1. Venezuela $24

2. Nigeria $83

3. Pakistan $113

4. Ukraine $140

5. Egypt $174

6. Albania $210

7. Malaysia $233

8. Iran $261

9. South Africa $277

10. Morocco $310

KU KARANTA: Akwai yiwuwar shugaba Buhari ba zai dawo ranar Lahadi ba, saboda ya na ganin likita

Idan ba a manta ba majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan dokar karin albashin ma'aikata zuwa naira dubu talatin, gwamnoni da dama a fadin kasar nan sunyi na'am da karin albashin, inda suka bayyanawa ma'aikatan su cewa a shirye suke su biya sabon albashin.

Mun ruwaito muku cewa wasu jihohi da suka hada da Kano, Zamfara, Kwara, Rivers, Kogi da Edo sun amince za su biya sabon albashin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel