Kasashe 37 da suke biyan albashi mafi yawa a 2019

Kasashe 37 da suke biyan albashi mafi yawa a 2019

- Majiyarmu LEGIT.NG ta yi kokarin kawo muku jerin kasashe a duniya da ma'aikatan su suka fi morewa da albashi

- Majiyar ta kawo muku kasashe 37 da suke samun albashi mafi tsoka a duniya

- Sai dai kuma wani abin haushin Najeriya ba ta samu damar shiga cikin jerin kasashen ba duk kuwa da karin albashin da aka yi a watan da ya gabata

A makonnin da suka gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan dokar karawa ma'aikata albashi daga naira dubu sha takwas zuwa naira dubu talatin a kowanne wata.

A hankali kuma ana samun gwamnoni da dama a kasar suna na'am da dokar, inda a yanzu ake sa ran kusan jihohi 30 ne suka yi maraba da sabon albashin, inda suka bayyanawa ma'aikatan su cewa a shirye suke domin su fara biyan sabon albashin.

Kasashe 37 da suke biyan albashi mafi yawa a 2019

Kasashe 37 da suke biyan albashi mafi yawa a 2019
Source: Getty Images

Hakanne kuma ya sanya majiyarmu LEGIT.NG ta yi wani bincike inda ta tattara jerin wasu kasashe a duniya wadanda suke biyan albashi mafi yawa a wannan shekarar ta 2019.

Majiyarmu ta samu damar tattara kasashe 37 a duniya, sai dai abin bakin cikin shine Najeriya ba ta cikin jerin kasashen duk kuwa da karin albashin da aka yi.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar shugaba Buhari ba zai dawo ranar Lahadi ba, saboda ya na ganin likita

Bisa ga rahoton da mujallar CEO World ta wallafa, kasar Australia ce ta fi biyan albashi mafi yawa, inda ta ke biyan ma'aikatan ta $14.14 a kowacce sa'a daya, daga ita kuma sai kasar Luxemborg da ke biyan $13.14 a kowacce sa'a.

Ga jerin kasashen da kuma yawan kudaden da suke biyan ma'aikatan su a kowacce sa'a daya:

1. Australia $14.14

2. Luxembourg $13.14

3. New Zealand $11.28

4. France $11.24

5. Netherlands $11.01

6. Ireland $10.87

7. Belgium $10.78

8. Germany $10.06

9. United Kingdom $9.74

10. Canada $9.06

11. Japan $7.61

12. United States $7.31

13. South Korea $6.71

14. Slovenia $5.51

15. Spain $5.07

16. Malta $4.9

17. Portugal $3.97

18. Greece $3.86

19. Estonia $3.38

20. Poland $3.24

21. Czech Republic $3.16

22. Slovakia $3.14

23. Croatia $3.03

24. Hungary $2.92

25. Latvia $2.89

26. Argentina $2.88

27. Turkey $2.87

28. Romania $2.84

29. Luthania $2.79

30. Macedonia $1.83

31. Serbia $1.8

32. Bulgaria $1.79

33. Brazil $1.43

34. Albania $1.17

35. Russia $0.94

36. Ukraine $0.84

37. Moldova $0.77

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel