In da ranka: An samu wata macijiya mai ido uku (Hoto)

In da ranka: An samu wata macijiya mai ido uku (Hoto)

A wani lamari da ba kasafai aka saba gani ko jin ya faru ba, an samu wata macjiya mai idanuwa guda uku a arewacin kasar Australiya.

Hukumomi da suka hada da hukumar rayar gandun daji a arewacin kasar ta Australiya (Northern Territory) sun tabbatar da labarin macijiyar da aka gani a kan wani babban titi.

Hukumar raya gandun dajin tayi magana ne bayan hotunan macjiyar ya fantsama a yanar gizo, musamman dandalin sada zumunta.

Sai dai macijiyar, wadda aka sanya wa suna Monty Python, ta mutu tun tana jaririya; makonni kadan bayan da aka gano ta a cikin watan Maris.

Masana kimiyya, musamman masu nazarin halittar dabbobi, sun bayyana cewar idon macijiyar na uku, wanda ke tsakiyar kan ta, ido ne da ya samu sakamakon sauyin halitta, a saboda haka ido ne na ainihi.

In da ranka: An samu wata macijiya mai ido uku (Hoto)
Macijiya mai ido uku
Asali: Twitter

Wasu masu yawon bude ido ne suka gano macijiyar a wani daji dake daf da garin Humpty Doo mai nisan kilomita 40 daga kudu maso gabashin birnin Darwin.

DUBA WANNAN: Za a samu karuwar marasa aikin yi a Najeriya - FG

An ga macijiyar, mai tsawon inci 15, a lokacin da take gararambar neman abinci a kan titin da ya ratsa ta cikin jejin da aka haife ta.

Hukumar gandun daji ta bayyana cewar macijiyar ba kawuna biyu gare ta ba tare da yin karin bayanin cewar akwai wata jijiya mai rai dake rike da idonta na uku, wanda ke tsakiyar kan ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel