Kungiyar Liverpool ce kadai a Ingila ta gagari Messi a kungiyoyin kasar Ingila
A ranar Laraba, 1 ga watan Mayu, 2019, kungiyar kallon kafan kasar Ingila, Liverpool, zata ziyarci takwararta, Barcelona, a wasan zagayen kusa da na karshe a garsar cin kofin zakarun nahiyar Turai (UCL).
Kungiyar Barcelona ta doke takwararta, Manchester United, a wasan zagaye na karshe kafin wannan. A wasa na karshe da kungiyar Manchester United ta ziyarci kasar Spain, kungiyar Barcelona ta zura kwallo uku a ragar Manchester United.
Dan wasan gaba na kungiyar Barcelona, Lionel Messi, ya zura kwallo biyu daga cikin ukun da kungiyar Barcelona ta ci.
A wata kididdiga da aka yi, an gano cewar Messi ya zura jumullar kwallo 24 a ragar kungiyoyin kasar Ingila da suka hada da Manchester City, Manchester United, Chelsea, Arsenal da Tottenham.
Amma wani abun mamaki shine, Messi bai taba zura kwallo a ragar kungiyar Liverpool ba duk da sun hadu a wasannin gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.
Messi ya zura kwallo 9 a ragar Arsenal a kara wa 6 da kungiyar tayi da kungiyar Barcelona a haduwar su na baya. Kazalika ya zura kwallo kwallo 3 a ragar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a kara wa 10 da suka yi da kungiyar Barcelona a baya.
DUBA WANNAN: Mohammed Salah zai tashi daga Liverpool, zai fadi kulob din da zai koma
A haduwa 6 da kungiyar Manchester City da Barcelona suka yi, Messi ya zura kwallo 6 a ragar kungiyar ta Manchester City. Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Machester United, kwallo 4 ya zura mata a raga a haduwa 6 da suka yi a baya.
A haduwa 2 da aka yi tsakanin Barcelona da Tottenham, Messi ya zira kwallo biyu a ragar kungiyar Tottenham, amma a wasanni biyu da ya buga tsakanin kungiyar Barcelona da Liverpool, Messi bai iya cin kwallo ko daya ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng