Karuwanci babban zunubi ne a koyarwar addinin Islama da na Kirista - Abayomi Shogunle

Karuwanci babban zunubi ne a koyarwar addinin Islama da na Kirista - Abayomi Shogunle

Shugaban cibiyar karbar korafin al'umma, Abayomi Shogunle, ya bayyana cewa sana'ar karuwanci ta sabawa koyarwar manyan addinai biyu na Islama da kuma na Kirista da suka kasance mafiya rinjaye a tsakanin al'ummar garin Abuja.

Shogunle ya yi Allah wadai da wadanda ke sukar yadda matakin doka ya muzgunawa masu sana'ar karuwanci a garin Abuja. Ya yi gargadin cewa sana'ar karuwanci na cin karo da duk wata doka ta tabbatar da da'a a kasar nan.

Ya yi kira na janyo hankali da cewar bincike ya tabbatar da yadda sana'ar karuwanci ta zamto ummul aba isin yaduwar cutar kanjamau da sauran cututtuka masu yaduwa ta hanyar saduwa a tsaknain al'ummar Najeriya.

Karuwanci babban zunubi ne a koyarwar addinin Islama da na Kirista - Abayomi Shogunle
Karuwanci babban zunubi ne a koyarwar addinin Islama da na Kirista - Abayomi Shogunle
Asali: Facebook

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Shogunle ya ce sana'ar karuwanci na haifar da tasiri wajen yaduwar wasu miyagun laifuka masu haddasa tarzoma da tayar da zuane tsaye a tsakanin al'umma.

Shogunle wanda ya kasance mataimakin kwamishinan 'yan sanda ya bayyana hakan ne a shafin sa na dandalin sada zumunta yayin babatun cewa, masu sana'ar karuwanci ba sa amfanar da kasa ta hanyar biyan haraji illa iyaka kawo zagon kasa a gare ta.

Wannan lamari ya biyo bayan hukuncin da wata kotun tafi da gidan ka ta zartar na yanke hukuncin daurin zama a gidan dan Kande na tsawon wata guda kan wasu Mata 27 da aka kama da laifin sana'ar karuwanci a garin Abuja.

KARANTA KUMA: Buhari yana yabawa jajircewa da kwazo bisa aiki - Omoboriowo

Alkaliyar kotun Jennifer Ogbogu, yayin zartar da hukuncun ta kan Matan da aka cafke a tsakanin ranakun Laraba da Alhamis na makon da ya gabata, ta ba su zabin biyan tara ta kimanin Naira dubu uku a kan kowane daya daga cikin su.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, da yawa daga cikin al'ummar Najeriya musamman masu ribatar dandalan sada zumunta sun bayayna rashin jin dadin su dangane da wannan lamari da a mahangar su ya kasance wata hanya ta dakilewa Mata 'yanci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel