Ministan Shari’a ya fayyace maganar maida albashi akalla N30, 000

Ministan Shari’a ya fayyace maganar maida albashi akalla N30, 000

Mun fahimci cewa babu abin da ya rage wajen fara biyan Ma’aikatan Najeriya sabon tsarin albashi bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kudirin karin albashi a Najeriya.

Vanguard ta rahoto cewa babu abin da ya ragewa Ma’aikatu da Hukumomi wajen biyan N30, 000 a matsayin mafi karancin albashin Ma’aikata. Gwamnatin Tarayyar tayi wannan karin bayani ne a jiya 27 ga Watan Afrilun 2019.

Ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami SAN ne yayi wannan jawabi a karshen makon nan inda ya bayyana cewa ba tare da bata lokaci za a fara biyan Ma’aikata mafi karancin albashin da shugaban kasa ya sa wa hannu ba.

KU KARANTA: Rashin aikata ya sa Ma'aikatan Jihar Kogi sun koma bara

Ministan Shari’a ya fayyace maganar maida albashi akalla N30, 000
Minista Malami yace babu abin da zai hana a fara biyan sabon albashi
Source: Depositphotos

Abubakar Malami yayi wannan jawabi ne a daidai lokacin da labarai ke yawo cewa har yanzu ana jira Ma’aikatarsa ta shari’a ta kammala wasu ayyuka kafin a karawa Ma’aikata albashi, duk an amince da kudirin karin albashi a kasar.

Malami yake cewa za a fara biyan wannan kudi ba tare da ya amince da komai daga ofishin sa ba. Ministan yace da zarar shugaban kasa ya sa kudirin karin albashin cikin dokar kasa, abin da za a jira kurum shi ne karshen wata yayi.

A cewar Ministan, babu abin da ya shafi ma’aikatarsa da karin albashi illa iyaka kurum Ma’aikatan gwamnati da ke da wannan alhaki su cika umarnin da shugaban kasa ya bada. Wannan akasin jita-jitan da ke yawo ne a kafofin labarai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel