Kasar Iran ta yaba ma Buhari da ya bari El-Zakzaky ya samu ganin likitoci daga waje

Kasar Iran ta yaba ma Buhari da ya bari El-Zakzaky ya samu ganin likitoci daga waje

Gwamnatin kasar Iran ta yaba ma gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta bari tawagar likitoci daga waje suka duba Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, Shugaban kungiyar yan Shi’a na Najeriya da matarsa.

A wani jawabi da aka saki a ranar Asabar, kakakin ma’aikatar Iran, Seyed Abbas Mousavi, ya nuna yakinin cewa hakan zai bude dammar tattaunawa tsakanin hukumomin kungiyar Shi’a a Najeriya da gwamnatin Najeriya.

Wata tawaga na kwararrun likitoci a ranar Alhamis sun kamala gwaje-gwaje akan lafiyar babban shehun malamin, Sheikh Zakzaky da matarsa wadanda suka dade a tsare tun a shekarar 2015.

Kasar Iran ta yaba ma Buhari da ya bari El-Zakzaky ya samu ganin likitoci daga waje

Kasar Iran ta yaba ma Buhari da ya bari El-Zakzaky ya samu ganin likitoci daga waje
Source: Facebook

Tawagar karkashin jagorancin hukumar kare hakkin musulmi na kasar Birtaniya (IHRC), sun ziyarci malamin da matarsa, Mallama Zeenah, a ranar Alhamis, sannan suka nemi yin binciken gaggawa akan lafiyarsu wanda ake ganin za a gudanar a yan kwanaki biyu masu zuwa.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sace gawa a Rivers, sun nemi N1m kudin fansa

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa likitocin sun samu damar ganawa da Zakzaky ne bayan samun umarni daga Alkalin wata babbar kotu dake jahar Kaduna, wanda ke sauraron karar da gwamnatin jahar Kaduna ta shigar da Zakzaky.

Duba da halin rashin lafiya da shugaban yan shi’an yake ciki ne yasa Alkalin ya umarci hukumar tsaron sirri wanda ke rike da Zakzaky da matarsa Zeenatu, dasu gaggauta gayyato masa likitocin da yake so don su duba lafiyarsa dana matar tasa.

Tunda fari dai lauyan Zakzaky, Femi Falana ne ya nemi wannan bukata daga Alkalin kotun, bayan ya bata bayanin cewa har yanzu Zakzaky da matarsa suna fama da matsanancin ciwo sakamakon raunuka da suka samu daga harbin bindiga da Sojoji suka yi musu a yayin da suke kokarin kamasu a shekarar 2015.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel