Gwamna El-Rufai ya sanya dokar hana shige-da-fice a Kaduna na sa’o’i 24

Gwamna El-Rufai ya sanya dokar hana shige-da-fice a Kaduna na sa’o’i 24

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya sanar da sanya dokar ta baci da zata hana shige da fice gaba daya na tsawon awanni ashirin da hudu a yankin garin kasuwar Magani.

Legit.ng ta ruwaito mukaddashin gwamnan jahar, Barnabas Bala Bantex ne ya sanya wanna dokar ta baci a yankin na kasuwar magani, kamar yadda kaakakin gwamnatin jahar, Malam Samuel Aruwan ya tabbatar da safiyar Juma’a, 26 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Gwamnati za ta biya kaakakin majalisa N500,000 duk wata a matsayin fansho

Haka zalika sanarwar ta kara da cewa wannan doka na shige da fice na tsawon awanni 24 ya shafi kafatanin karamar hukumar Kajuru, wanda dama an dade ana samun matsalar tsaro daya shafi kai ma jama’a hare hare ba tare da sun aikata laifin fari ba balle na baki.

Mukaddashin gwamnan jahar Kaduna ya bayyana cewa dokar ta fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba, sa’annan yayi kira ga dukkanin jami’an tsaro da hakkin tabbatar da zaman lafiya a yankin ya rataya a wuyansu dasu tabbata sun yi aiki tukuru don tabbatar da ganin jama’a sun bi wannan doka.

Daga karshe kuma Bantex yayi kira ga jama’an garin Kasuwar magani da na karamar hukumar Kajuru kwata dasu baiwa jami’an tsaro hadin kai, kuma su yi zamansu a gida har sai an samu cigaban tsaro a yankin, saboda a cewarsa gwamnati ta dauki wannan mataki ne don karesu da dukiyoyinsu.S

Duka duka bai wuce wata daya ko sama da hakan kadan ba da gwamnatin jahar Kaduna ta janye dokar ta bacin da ta kakaba a garin kasuwar magani ba, hakan ya biyo zaman lafiyan da aka samu ne a yankin, sai gashi a yanzu rikici ya sake barkewa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel