Babban bankin duniya ta ware $5,000,000 don gudanar da wasu manyan ayyuka 2 a Katsina

Babban bankin duniya ta ware $5,000,000 don gudanar da wasu manyan ayyuka 2 a Katsina

Babban bankin duniya ta ware dalan amurka miliyan biyar ($5,000,000), kimanin naira biliyan daya da miliyan dari takwas (N1,800,000,000) kenan don gudanar da wasu muhimman aiki a jahar Katsina guda biyu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito bankin duniyan zata gudanar da aikin magance matsalar zaizayar kasa tare da aikin magance matsalar ambaliyan ruwa ne a jahar ta Katsina, kamar yadda shugaban aikin, Dakta Amos Abu ya bayyana.

KU KARANTA: Matashi ya kashe kansa bayan wani sabani tsakaninsa da budurwarsa

A jawabin a garin Katsina, Dakta Amos, a yanzu haka ana gudanar da wadannan ayyuka a jahohi 20 na Najeriya, amma jahar Katsina za ta samu kulawa na musamman sakamakon yadda matsalar ta addabi jahar.

Ya bayyana tsarin gudanar da aikin, inda yace jahohi zasu samar da wani kaso na kudaden daga aljihunsu, sai bankin ta basu karin tallafin kudi daga bangarensu, wanda da jimillan kudin ne za’a gudanar da aikin.

Shima da yake nasa jawabi, gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana cewa akalla al’ummomi 3,000 ne suka mika kokon bararsu ga gwamnatin jahar don neman ta magance musu matsalolin zaizayar kasa dana ambaliya.

Sai dai gwamnan yace zuwa yanzu jahar Katsina ta kashe makudan kudi da suka kai naira biliyan shida wajen shawo kan matsalolin muhalli da suka fitini wasu yankunan jahar da yawansu ya haura 150 a duk fadin jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng