Matashi ya kashe kansa bayan wani sabani tsakaninsa da budurwarsa

Matashi ya kashe kansa bayan wani sabani tsakaninsa da budurwarsa

Wani matashi dan shekara 29 dake aikin tuka kwale kwale a jahar Bayelsa, Alabo Enai ya kashe kansa sakamakon bacin ciki daya turnukeshi bayan samun wata yar sabani tsakaninsa da budurwarsa Blessing.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito saurayi Alabo dan asalin karamar hukumar Brass na jahar Bayelsa ya samu matsala ne da budurwarsa Blessing yar kabilar Ologbobiri na karamar hukumar Ijaw ta kudu, wanda hakan ta kai ga alakarsu tana tangal tangal.

KU KARANTA: Kungiyar kwadago ta dauki alwashin tursasa gwamnoni biyan karancin albashin N30,000

Duk kokarin da saurayin yayi na shawo kan budurwarsa yaci tura, wanda hakan yayi sanadiyyar kashe kansa inda yayi amfani da ragar kama kifi ya daure wuyarsa daga saman bishiya, abin mamaki kuma wannan budurwa Blessing ce ta gano gawarsa a rataye.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa “Nan da nan jama’a suka taru suna kallon gawartasa tare da mamakin dalilin daya kaishi ga aikata hakan, gashi kuma bai bar wani sako ba, daga bisani ta bayyana mana cewa sun samu matsala dashi, watakila hakan ne yasa ya dauki wannan mataki akansa.”

Ita ma budurwa tayi karin haske kamar haka “Matsalar da muka samu itace na fada masa ina so na koma garinmu a kudancin Ijaw, shi kuma bai amince da hakan ba, amma da naga ranshi ya baci sai na hakura mu cigaba da zama tare, a wannan ranar daya mutu sai da nace masa yazo mu tafi wasan Easter, amma yaki, yace na tafi kawai.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, SP Asinim Butswat ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma yace tuni jami’an Yansanda suka kaddamar da bincike akan lamarin don tabbatar da babu wata lauje cikin nadi.

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel