'Yan Shi'a sun kutsa kai cikin dakin majalisar wakilai a Abuja
- An tilastawa 'yan majalisar wakilai na tarayya daga taron su, bayan 'yan shi'a masu zanga-zanga da ke Abuja sun kutsa kai cikin dakin taron majalisar da ke Abuja
- 'Yan shi'an wadanda suka shafe shekaru suna zanga-zanga da nuna bukatar gwamnati ta saki jagoransu, bayan kama shi da ta yi a watan Disambar shekarar 2015
A jiya Laraba ne 24 ga watan Afrilu, majalisar wakilai ta tarayya dakatar da zaman da ta ke yi babu shiri, jim kadan bayan 'yan shi'a masu zanga-zanga sun kutsa kai cikin dakin majalisar ta karfin tsiya.
Mataimakin kakakin majalisar wakilai na kasa, Yusuf Lasun, ya ce 'yan shi'ar wadanda suke gabatar da zanga-zanga sun karya kofar shiga majalisar ta farko suka kutsa kai cikin dakin majalisar. Hakanne ya tilasta majalisar dakatar da zaman da ta ke yi.

Asali: Facebook
'Yan Shi'an sun gudanar da zanga-zanga babu adadi a fadin kasar nan, suna bukatar gwamnati ta saki jagoransu, wanda ta kama tun watan Disambar shekarar 2015.
An kama shugaban na su, Ibrahim El-Zakzaky, tare da matarsa Zeenaat, bayan sojoji sun kashe daruruwan 'yan shi'ar a Zaria, jihar Kaduna, a tsakanin 12 ga watan Disamba zuwa 15 ga watan Disambar shekarar 2015. Wasu daga cikin 'ya'yan El-Zakzaky suma sun mutu sakamakon zuwan sojojin.
KU KARANTA: Ya kashe 'yan uwar budurwarshi su takwas saboda ta ce ba ta son shi
Akalla mutane 347 ne aka tabbatar da mutuwarsu kuma an binne su a Kaduna.
Har ya zuwa yanzu El-Zakzaky da matarsa Zeena, na nan a tsare, bisa zargin da ake yi musu na kashe soja.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng