Asibitin koyarwa na Jami'ar Danfodiyo ya fara tiyata a zuciya

Asibitin koyarwa na Jami'ar Danfodiyo ya fara tiyata a zuciya

Da sanadin kafar watsa labarai ta jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, asibitin koyarwa na jami'ar Danfodiyo da ke jihar Sakkwato wato birnin Shehu, cikin yalwar arziki na nasibi ya fara gudanar da tiyatar zuciya.

Yayin ganawar sa da manema labarai a birnin Sakkwato, mukaddashin shugaban asibitin Dakta Nasir Muhammad, ya ce cututtukan zuciya na neman zama ruwan dare a duniya da cikin kankanin lokaci ta ke kassara mai dauke da ita ba tare da ya farga ba.

Asibitin koyarwa na Jami'ar Danfodiyo ya fara tiyata a zuciya
Asibitin koyarwa na Jami'ar Danfodiyo ya fara tiyata a zuciya
Asali: Depositphotos

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, gogaggen likitan ya ce akwai fiye da mutane 5,000 da ke bukatar a aiwatar masu da tiyata a zuciya cikin jihohin Sakkwato, Kebbi da kuma Zamfara.

Dakta Nasiru ya hikaito yadda talakawa masu dauke da cututtukan zuciya ke shiga cikin halin ni 'ya su a sakamakon tsadar gudanar da tiyatar zuciya da tukwicin sa ya kai kimanin Naira miliyan biyar a kasar nan. Ya bayar da misali da asibitin Nizamiyya da ke garin Abuja.

Kazalika likitan ya ce ba ya ga rahusa a halin yanzu nesa ta matsanto kusa yayin da za a rika gudanar da tiyatar zuciya cikin asibitin koyarwa na jami'ar danfodiyo a kan mafi kankantar kudi na Naira miliyan biyu kacal domin kawo rahusa ga talakawa.

KARANTA KUMA: Gidauniyar Musulunci ta duniya ta gayyaci Sanata Wamakko taro a kasar Saudiya

A yayin da za a rika gudanar da tiyatar zuciya a asibitin tare da hadin gwiwar kwararrun lafiya na asibitin koyarwa na Sarki Muhammad VI da ke jami'ar kasar Morocco, Dakta Nasiru ya nemi tallafin gwamnati, hamshakan kungiyoyi masu zaman kansu wajen goyon bayan wannan muhimmin lamari da aka farar cikin yankin Arewa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng