Manyan jiragen ruwa 28 zasu sauke man fetir da kayan masarufi a tashoshin Legas

Manyan jiragen ruwa 28 zasu sauke man fetir da kayan masarufi a tashoshin Legas

Akalla jiragen ruwa guda 28 ne suke tafe daga kasashen waje suka nufo Najeriya domin sauke man fetir da sauran kayayyakin masarufi a tashoshin jiragen ruwan Najeriya dake cikin jahar Legas, yankin kudu masu yammacin kasar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jiragen zasu fara sauke kayan da suka dauko ne daga ranar 23 ga watan Afrilu zuwa ranat 2 ga watan Mayu a tashohin jiragen ruwa na tsibirin Tin Can da kuma Apapa.

KU KARANTA: Zargin Buhari na barci akan aiki: fadar shugaban kasa ta mayar ma Fasto da martani

Daga cikin jiragen dankaron guda ashirin da takwas, Tara daga cikinsu na dauke da tataccen man fetir, yayin da sauran guda goma sha tara ke dauke da siga, daskararren kifi, fulawa, kayan karfe, da kuma sundukia dake dauke da kayan amfanin yau da kullum da dama.

A cewa hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya, NPA, tuni jirage shida daga cikin ashirin da takwas suka isa tashoshin jiragen ruwan Najeriya, kuma suna dakon samun izinin sauke man fetirin da suka dauko.

A wani labarin kuma, shugaban cibiyar tuntuba ta tashoshin jiragen Najeriya, PCC, Cif Kunle Folarin ya nemi gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen shawo kan cunkoson ababen hawan da ake samu a titunan da suka shiga cikin tashoshin.

A cewarsa, fadada titunan ya zama wajibi don baiwa motocin dake safa da marwa akansu damar wucewa cikin ruwan sanyi ba tare da sun fuskanci matsalar cunkoson ababen hawa saboda rashin kyawun hanya ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel