Macizai sun hana shugaban kasar Liberia aiki a ofishin sa

Macizai sun hana shugaban kasar Liberia aiki a ofishin sa

Wasu bakaken Macizai biyu sun fatattaki shugaban kasar Liberia, George Weah daga ofishin sa. Hakan ya sanya ta dole shugaban kasar ya ke gudanar da aiki na rike akalar jagorancin kasar daga farfajiyar gidan sa.

Shugaban kasar Liberia da ya kasance tsohon dan kwallon kafa mai rike da kambun gwanin shekara na duniya, ya turke kansa cikin gida tun a ranar Larabar da ta gabata inda ya ke gudanar aiki sakamakon wasu macizai biyu da suka sulala cikin ofishin sa.

Shugaban kasar Liberia; George Weah

Shugaban kasar Liberia; George Weah
Source: Getty Images

Babban sakataren sadarwa na fadar gwamnatin kasar Liberia, Mista Smith Toby, ya shaidawa manema labarai na BBC cewa, an yi kacibus da wasu macizai biyu a ma'aikatar harkokin kasashen ketare inda shugaban kasa Weah ya ke gudanar da ayyukan sa.

A sanadiyar wannan lamari fadar gwamnatin kasar ta bayar da umurni ga ma'aikata da su kauracewa ofishin har zuwa ranar 22 ga watan Afrilu domin tabbatar da ya tsarkaka daga wannan muguwar dabba.

KARANTA KUMA: An kone 'Daliba kurmus bayan ta tona asirin shugaban makaranta da laifin keta mata haddi

Makamanciyar haka ta kasance a nan gida Najeriya, inda wasu Beraye suka hana shugaban kasa Muhammadu Buhari kusantar ofishin sa har na tsawon kwanaki bayan dawowar sa daga jinya ta kimanin tsawon watanni uku a birnin Landan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel