An kone 'Daliba kurmus bayan ta tona asirin shugaban makaranta da laifin keta mata haddi

An kone 'Daliba kurmus bayan ta tona asirin shugaban makaranta da laifin keta mata haddi

A can kasar Bangladesh, wata daliba ta yi gamo da azal na rayuwa, inda aka kone ta kurmus bisa ga umurnin shugaban makaranta bayan ta tona masa asiri na laifin keta mata haddi kamar yadda hukumar 'yan sanda ta bayyana a ranar Juma'a.

'Yan sandan kasar Bangladesh

'Yan sandan kasar Bangladesh
Source: UGC

Mutuwar wannan budurwa mai shekaru 19 kacal a duniya, Nusrat Jahan Rafi, ya haifar da mummunar zanga-zanga a yankin kasar dake nahiyyar Kudancin Asia. Firai Ministan kasar, Sheikh Hasina ya sha alwashin hukunta dukkanin masu hannu cikin wannan zalunci.

Bayan da masu hannu cikin wannan muguwar aika-aika sun gaza samun biyan bukata yayin da suka nemi Nusrat ta janye korafin keta mata haddi, sun yi mata wanka da makamashi na Kalanzir kuma suka kone kurmus.

Hukumar 'yan sanda yayin karin haske dangane da wannan lamari na takaici ta bayyana cewa, ta samu nasarar cafke mutane 17 ababen zargi inda daya daga cikin su ya amsa laifi sa da cewa sun aikata hakan ne bisa umurni na shugaban makaranta.

Babban jami'in dan sanda mai gudanar da bincike a kan wannan mugun ji da mugun gani, Muhammad Iqbal, ya shaidawa manema labarai na jaridar AFP cewa, Nusrat ta riga mu gidan gaskiya a ranar 10 ga watan Afrilu inda ba ta gushe ba wajen ci gaba da bayyana koke a kan shugaban makarantar da ya keta mata haddi.

KARANTA KUMA: Yawan ta'ammali da gishiri na haifar da rashin lafiyar Hanta a jikin dan Adam

Jagorar kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasar, Meenakshi Ganguly, yayin babatu na neman a tabbatar da yiwa Nusrat adalci tare da nema mata hakki, ta kuma bayyana yadda gwamnatin kasar Bangladesh ta gaza ta fuskar kare al'umma daga cin zarafi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel