Kujerar shugaban majalisar dattawa: Danjuma Goje ne zabin mu - Kungiyar Arewa maso Gabas

Kujerar shugaban majalisar dattawa: Danjuma Goje ne zabin mu - Kungiyar Arewa maso Gabas

Kungiyar Arewa maso Gabas NECF, North East Consultative Forum, tare da wasu kungiyoyi biyar na yankin, sun bayyana goyon bayan su ga Sanata Muhammad Danjuma Goje, a matsayin wanda su ke son ya kasance sabon shugaban majalisar dattawa.

Sanata Muhammad Danjuma Goje

Sanata Muhammad Danjuma Goje
Source: Depositphotos

Kungiyoyi biyar da ke goyon bayan kudirin NECF wajen kasancewar Goje a matsayin sabon shugaban majalisar dattawa sun hadar da; kungiyar dattawan Arewa maso Gabas, kungiyar kusoshin jam'iyyar APC, kungiyar zauren tattanawa ta jihar Borno kungiyar 'yan siyasar jihar Gombe da kuma kungiyar matasa masu akidar jagoranci na gari.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, kungiyoyin sun yi tarayya wajen yanke wannan shawara yayin zaman ganawa da juna da suka gudanar cikin jihar Bauchi a ranar Laraba,17 ga watan Afrilun 2019.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa,bisa ga hukunci na shawara da kungiyoyin suka zartar, sun ce Sanata Goje ya kasance mafifici ta fuskar cancantar zabi cikin Sanatoci uku manema kujerar jagoranci a sabuwar majalisar dattawa.

KARANTA KUMA: Nasara ta mu ce a zaben gwamnan jihar Kogi - PDP

A sanadiiyar haka kungiyoyin a ranar Larabar da ta gabata sun aike da wata rubutacciyar wasika zuwa ga shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, domin zayyana masa shawarar da suka yanke.

Cikin wasikar, kungiyoyin sun bayyana bajintar Sanata Goje ta fuskar gudunmuwa mai girman gaske da ya bayar a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tun yayin kafuwar ta a 2015 da kuma taka rawar gani wajen samun nasarar jam'iyyar APC a babban zabe na bana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel