Cin zarafin 'ya'yan ta: PDP ta janye zanga-zanga a jihar Kano

Cin zarafin 'ya'yan ta: PDP ta janye zanga-zanga a jihar Kano

Jam'iyyar PDP reshen jihar Kano, ta janye zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a sakamakon cin zarafi, muzgunawa, wulakantaswa, keta haddi da kuma barazanar mutuwa da wasu hukumomin tsaro ke yiwa 'ya'yan ta a jihar.

Babban sakataren kwamitin kula da harkokin gudanarwa na jam'iyyar PDP reshen jihar Kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa tare da bayyana hukunci da dalilin janye kudirin zanga-zanga da jam'iyyar ta aiwatar.

Cin zarafin 'ya'yan ta: PDP ta janye zanga-zanga a jihar Kano

Cin zarafin 'ya'yan ta: PDP ta janye zanga-zanga a jihar Kano
Source: Twitter

Alhaji Sagagi ya yi bayanin cewa, duba da yadda aka samu rangwamin cin kashi da ake yiwa 'ya'yan ta, ya sanya uwar jam'iyyar ta yanke shawarar dakatar da zanga-zangar da kudirci gudanarwa domin bayyana damuwar ta.

Cikin sanarwar da Sagagi ya bayyana, gwamnatin jam'iyyar APC na ci gaba da ya yiwa wasu mashahuran 'ya'yan ta barazana ta cin zarafi da suka hadar da Hajiya Zainab Audu Bako, Hajiya Binta Speaking, Sanusi Bature Dawakin Tofa, Salisu Yahaya Hotoro, Babangida Bangis da makamantan su.

KARANTA KUMA: Buhari ya kira attajirin duniya Bill Gates, ya yaba masa a kan yakar cutar shan inna da kanjamau a Najeriya

Sakataren jam'iyyar ya yi Allah wadai dangane da yadda shugabancin jam'iyyar APC karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ke ci gaba da wulkantaswa tare da cin zarafin mambobin jam'iyyar ta hanyar dakile masu 'yanci da hakki na Bil Adama.

Sagagi ya buga misali da yadda hukumar DSS a ranar Talata ta sallamo Salisu Yahaya Hotoro da kuma Babangida bangis bayan tsare su har na tsawon kwanaki goma sha biyu ba tare da wani hakki ko dalili na laifin da su ka aikata ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel