Buharin dana sani a da, ba shi bane Buharin yanzu – Inji tsohon dogarin shugaba Buhari

Buharin dana sani a da, ba shi bane Buharin yanzu – Inji tsohon dogarin shugaba Buhari

Mai martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Haruna Mustapha Jokolo ya bayyana damuwarsa da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke gudanar da mulki a Najeriya, inda yace tabbas wannan ba Buharin da ya sani, kuma yayi aiki dashi bane a baya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sarki Jokolo wanda shi kansa tsohon Soja ne ya taba yin aiki da shugaba Buhari a zamanin mulkin Soja, inda ya kasance babban dogarinsa a lokacin da yake shugabancin kasar Najeriya a matsayin Soja.

KU KARANTA: Rikici a Kannywood: Amina Amal ta nemi diyyar naira miliyan 50 daga wajen Hadiza Gabon

Buharin dana sani a da, ba shi bane Buharin yanzu – Inji tsohon dogarin shugaba Buhari
Jokolo da Buhari
Asali: Facebook

Don haka Sarkin ya san Buharin ciki da bai, da wannan ne yasa yake ganin sammu wasu mutane suka yi ma shugaba Buhari don su cimma burinsu na juyashi yadda suke so kamar waina, kuma Sarkin, wanda ba’a sanshi da boye boye ba ya bayyana mutanen da ake kira da ‘Cabals’ a matsayin wadanda suka yi masa sammun.

“Nayi aiki da shugaba Buhari har sau biyu, a zamanin da yake gwamnan jahar Arewa maso gabas, da kuma lokacin da yake shugaban kasar Najeriya na Soja, don haka na san ba rago bane wajen tafiyar da al’amuran da suka shafi mulki.

“Amma tunda sammu ta kama Annabin Allah, wanene ba zai kamu ba? Don haka sammu mutanen Buhari suka yi masa, watau ‘Cabal’ da ma sauran miyagun abubuwa don su samu damar juyashi yadda sua ga dama. Ba Buharin dana sani bane.” Inji shi.

Jokolo ya kara fito da ra’ayinsa a fili inda yace tun da har uwargidar shugaban kasa ta yi masa nuni ga wasu mutane dake juyashi, ta tabbata akwai tuggun da ake shirya masa kenan, don haka yayi kira ga Buhari daya tuna rantsuwar da yayi da Al-Qur’ani ya sauke nauyin dake rataye a wuyansa.

Haka zalika Sarkin ya bayyana damuwarsa da furucin da ministan tsaro, Mansur Dan Ali yayi game da sa hannun sarakunan gargajiya a matsalar tsaron jahar Zamfara, inda ya bukaci ministan da lallai ya bayyana sunayen Sarakunan.

Daga karshe Sarki jokolo yayi kira ga jama’a dasu guji wulakanta Al-Qur’ani mai tsarki, kamar yadda ake zargin anayi a jahar Zamfara, inda yace babu yadda za’a samu zaman lafiya idan har ana wulakanta Qur’ani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel