Tsaffin shugabannin majalisa 2, tsohon kakakin majalisar wakilai, tsaffin gwamnonin PDP sun marawa Ahmad Lawan baya

Tsaffin shugabannin majalisa 2, tsohon kakakin majalisar wakilai, tsaffin gwamnonin PDP sun marawa Ahmad Lawan baya

Zawarcin kujerar shugaban majalisar dattawan Najeriya ya dau sabon salo yayinda wasu tsofin shugabannin majalisar dattawa biyu da tsohon kakakin majalisar wakilai daya suke bayyana goyon bayansu wa Sanat Ahmad Lawan.

Kana wasu tsofin gwamnan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suna goyon bayan Lawan.

Binciken jaridar The Nation ya nuna cewa wasu tsofin shugabannin majalisar dattawan Najeriya biyu, tsohon kakakin da tsofin gwamnonin PDP (an sakaye sunayensu) suna goyon Ahmad Lawan bisa ga bukatar majalisa mai karfi.

Wasu daga cikin tsofin gwamnonin sun ce dalilin da yasa suke goyon bayansa shine irin alaka mai kyau da suke da shi a shekarun baya.

Tsofin shugabannin majalisar dattawan sun bayyana cewa Ahmad Lawan dan majalisa ne da ya samu kwarewa a aikin sosai.

KU KARANTA: Kashi 90 cikin 100 na shinkafan da ake ci, a kasar nan ake nomawa - Ministan Noma

Majiya mai karfi ya bayyana cewa: "Aikin da aka baiwa Lawan da sauran yan majalisun APC na tuntubar manyan yan siyasa da abokan hamayya ya fara haifan da mai ido."

"Akalla tsaffin shugabannin majalisar dattawa biyu, tsohon kakaki daya, kimanin tsofin gwamnonin PDP biyu da wasu tsofin ministocin PDP suna goyon bayan Lawan. Sun amince da cewa zaben Lawan shi yafi alkhairi ga majalisar dattawa."

"Wadannan shugabanni sun umurci mabiyansu su yiwa Lawan aiki saboda ana bukatar majalisar dattawa mai karfi. Kana sun yarda cewa majalisar ta fara rauni."

"Idan lokaci yayi, wadannan shugabanni zasu bayyana goyon bayansu a fili."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel