Gwamnati ta garkame gidajen mai 6 dake boye man fetir a Sakkwato
Hukumar kula da albarkatun man fetir, DPR, ta garkame wasu gidajen mai guda shida dake jahar Sakkwato da jahar Kebbi sakamakon kamasu da laifin boye man fetir da nufin sabbaba wahalarsa, tare da tsawwala farashin litan man.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban sashin zagaye na hukumar DPR, Muhammad Makera ne ya sanar da haka a ranar Talata yayin da yake yawon rangadin gidajen mai dake cikin birnin Sakkwato.
KU KARANTA: Zargin taron dangi a Kaduna: Karya kake mana – hukumar INEC ga Shehu Sani
A jawabinsa, Makera yace gidajen man suna sayar da man fetir fiye da farashin da gwamnati ta tsayar na N145, yayin da wasu daga cikinsu kuma suka tara dubun dubatan litocin mai suka boye da nufin sabbaba wahalar mai, ta yadda zasu samu riba mai yawa.
Baya ga matakib garkame gidajen man guda shida, kwanturola Muhammad Makera ya bayyana cewa sun ci su taran kudi naira dubu dari dari (N100,000) akan kowanne famfon mai da suke dashi a gidan man.
Ya kara da cewa babu wani dalili da zai sa jama’a su dinga sayen mai suna boyewa don tsoron wahalar man fetir, saboda a cewarsa akwai isashshen mai a kasa, inda ko a ranar Talata sai da aka shigo da tankunan mai guda 20 jahar Sakkwato, goma sha biyu daga cikinsu a birnin Sakkwato za’a saukesu.
Daga karshe ya bada tabbacin zasu cigaba da aiki tukuru don tabbatar da gidajen main a bin doka da ka’ida wajen sayar da man da suka sauke. Sa’annan rahotanni sun bayyana cewa layukan mai sun fara bacewa sakamakon gidajen mai suna sayar da mai.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng