Yadda jarrabawar bana ke kasancewa - JAMB
Hukumar JAMB mai kula da shiryawa dalibai jarrabawar neman shiga jami'o'i a Najeriya ta ce za ta jajirce wajen tabbatar da kyakkyawan sakamako yayin da ake ci gaba da gudanar da jarrabawar cikin inganci da nagarta a bana.
Shugaban sadarwa da hulda da al'umma na hukumar, Dakta Fabian Benjamin, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata hira yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata cikin babban birnin kasar nan na tarayya.
Dakta Benjamin ya ce a yayin da kimanin fiye da dalibai miliyan 1.2 manema shiga jami'o'i suka zana jarrabawar JAMB a bana daga ranar Alhamis 11 ga watan Afrilun 2019 kawowa yanzu, za a karkare jarrabawar a ranar Laraba 17 ga watan na Afrilu.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, ana sa ran fiye da dalibai miliyan 1.8 manema shiga jami'o'i a fadin Najeriya za su zana jarrabawar JAMB a bana da ta fara gudana a makon da ya gabata.
KARANTA KUMA: Buhari zai tsananta yaki da rashawa a wa'adi na biyu - Lai Mohammed
A yayin da ba bu wata babbar tangarda da hukumar JAMB ta fuskanta a bana inda jarrabawar ke gudana cikin nagarta da inganci a bana, Dakta Benjamin ya ce kawowa yanzu ba bu sakamakon jarrabawar ko wane dalibi da ta saki.
Babban jami'in na hukumar JAMB ya yi karin haske dangane da yadda ake ci gaba da tantance sakamakon jarrabawar biyo bayan aukuwar wasu ababe na zamba cikin aminci da aka cafke yayin gudanar ta.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng