Wani dan shekara 55 ya lalata yarinya yar shekara 8

Wani dan shekara 55 ya lalata yarinya yar shekara 8

- Wata kotun Majistare da ke Makurdi ta daure wani ma’aikaci dan shekaru 55 a Benue

- An tsare mai laifin ne kan zargin yiwa yar shekara 8 fyade

- An garkame mai laifin ne a Kurkukun Tarayya da ke Makurdi bayan sauraran karan

Wata kotun Majistare da ke Makurdi ta daure wani ma’aikaci dan shekaru 55 a Benue, mai suna Samuel Lornav, a ranar Juma’a bisa laifin yiwa yar shekara 8 fyade.

Mai shari’a, Misis J.O Ayia, ta ba da umurnin cewa a rufe mai laifin a Kurkukun Tarayya da ke Makurdi bayan sauraran karan.

Wani dan shekara 55 ya lalata yarinya yar shekara 8

Wani dan shekara 55 ya lalata yarinya yar shekara 8
Source: UGC

Dan sanda mai gabatar da kara, Mista Ato Godwin, ya fada ma kotun cewa Emmanuel Ejeh, wanda ke sa zama a bayan ofishin hukumar NUJ, a Makuradi ne ya kawo rahoton lamarin zuwa ga ofishin yan sanda a ranar 8 ga watan Afrilu, 2019.

An rahoto cewa mai laifin ya yiwa yarinyar fyade da karfi da yaji, ya kuma karbi bakin kan aikata laifin.

KU KARANTA KUMA: Fashi: Ministan tsaro yace furucinsa baya nufin kaskanta sarakunan gargajiya

Yayinda aka gabatar da karan, ba a amsa rokon mai laifin ba.

Mai gabatarwan ya bayyana cewa har wa yau dai ana kan gudanar da bincike kan lamarin, ya bukaci kotun da ta sake sa rana don cigaba da sauraran karan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel