Yanzu Yanzu: An sulhunta Ali Nuhu da Adam Zango

Yanzu Yanzu: An sulhunta Ali Nuhu da Adam Zango

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an yi sulhu a tsakanin manyan fitattun jaruman nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa, wato Ali Nuhu da Adam A. Zango a garin Kano, bayan gumurzun da suka tafka.

Hadakar kungiyar nan ta masu shirya fina-finan Hausa ta kasa wacce aka fi sani da MOPPAN karkashin jagorancin Abdullahi Maikano ce ta yi nasarar shirya jaruman biyu.

Anyi hakan ne a ofishin jigon Kannywood kuma shugaban majalisar amintattu na kungiyar, wato Malam Abdulkarim Mohammed a yau Asabar, 13 ga watan Afrilu.

Yanzu Yanzu: An sulhunta Ali Nuhu da Adam Zango

Yanzu Yanzu: An sulhunta Ali Nuhu da Adam Zango
Source: Facebook

Sakataren kungiyar MOPPAN reshen jihar Kano, Malam Salisu Officer, ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya na mai cewa, yanzu Ali zai janye karar da ya kai Adamu a kotu.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Ali Nuhu ya yi karar Adam A Zango a kotu kan cewa kotu ta shiga tsakaninsa da Zango kuma ya daina ba ta masa suna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Sakkawato: Birnin Shehu; inda yara kanana ke fita domin neman aikin yi

Wannan na dauke ne cikin takardan kirar kara wanda Ali Nuhu ya shigar a kotun USC da ke Fagge a Kano.

Kotun ta bukaci Adam Zango ya gurfana gaban a ranar 15 ga watan Maris na 2019 misalin karfe 8.30.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel