Wata mata ta mutu a gidan boka, lokacin da ta je neman magani
Jami'an hukumar 'yan sanda jihar Kwara sun kama wani boka da zargin hannu a mutuwar wata mata mai shekaru 45 mai suna Mrs Tawakalitu Mukaila, inda aka samu gawarta a gidan shi.
An gano cewar matar ta mutu a gidan Emmanuel a Ila-Odo-Owa, karamar hukumar Oke-Ero, bayan Tawakalitu, ta hadu da Emmanuel a kasuwar Omu Aran, lokacin da ta ke gabatar da kasuwancin ta.
An samu bayanin cewa Emmanuel ya fadawa Tawakalitu cewa ita da iyalinta anyi musu asiri kuma suna bukatar taimakon gaggawa daga wurinshi. An gano cewa Emmanuel ya bayyanawa Tawakalitu wasu abubuwa da suka faru da ita da iyalanta, lokacin da ta ke zaune a Isale-Oyo a jihar Oyo.
Mijinta Munkaila, direba ne, dan garin Oke-Ode a jihar Kwara, ya samu hatsarin mota shekaru 4 da suka wuce, wanda yayi sanadiyyar gurguncewarshi, dole ya koma tafiya da abin dogarawa.
An gano cewa bayan matsa lamba da amfani da siddabaru, a karshe Emmanuel ya shawo kan Tawakalitu, inda ya jawo ta gidanshi ita da wata 'yar uwarta Azeezat mai shekaru 17 a duniya.
Mijin ya bayyana cewa, "ranar Alhamis kawai ya tashi ya nemi matar tashi ya rasa ita da Azeezat, abinda ya tada hankalinmu kenan, inda muka yi neman duniyar nan amma ba mu ganta ba."
Ya ce ranar Lahadi da safe sai ga Azeezat ta shigo, duk a rame, inda ta ke bayyana mana irin abubuwan da suka faru da su a gidan Emmanuel.
KU KARANTA: Atiku na cikin tsaka mai wuya
"Azeezat ta bayyana mana cewa kwanansu 3 a gidan bokan ita da Tawakalitu, ranar Asabar da safe ya bawa Tawakalitu wani magani ya ce ta sha.
"Tace bayan ta sha maganin Emmanuel ya bata wata kwarya ta yi amai a ciki. Bata jima da yin aman ba sai ta fara rashin lafiya, mintina kadan ta ce ga garinku nan."
Munkaila ya ce, Azeezat ta bayyana mishi cewar bayan mutuwar Tawakalitu, sai Emmanuel ya kulle su ita da marigayiyar a cikin wani daki, inda ya fada mata idan ta fadawa wani abinda ya faru ita ma za ta mutu.
"Azeezat ta ce ranar Lahadi da safe ne bayan yunwa da wahala ta samu ta bude dakin ta gudo ta bar gawar Tawakalitu a gidan bokan."
A yanzu haka dai hukumar 'yan sanda sun cafke Emmanuel, inda suke gabatar da bincike akan shi, kafin su mika shi zuwa kotu, domin ya ke mishi hukunci.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng