Kotu ta raba wani aure bayan shekaru 16 saboda cin amana

Kotu ta raba wani aure bayan shekaru 16 saboda cin amana

Wata babban kotun Shari'a da ke zamanta a Maraba a jihar Nasarawa ta katse igiyar aure tsakanin Samson Apaila da matarsa Grace bisa zargin cin amanar aure da yawan rikici tsakanin ma'auratan.

Alkalin kotun, Ibrahim Shekarau ya raba auren ne saboda a samu zaman lafiya tunda ma'auratan biyu sun ce ba za su iya cigaba da zama a matsayin mata da miji ba.

Shekarau ya bawa wanda ya shigar da karar damar kulawa da yaransu uku da suka haifa yayin zaman aure na shekaru 16.

Apaila ya shaidawa kotu cewa ya auri wanda akayi karar ne tun 2003 bisa al'adarsu na kabilar Igala kuma sun haifi 'ya'ya uku.

DUBA WANNAN: Khadimul islam: Ganduje ya rufe wani babban Otel a Kano, an kama masu karuwanci 19

Kotu ta raba wani aure bayan shekaru 16 saboda cin amana

Kotu ta raba wani aure bayan shekaru 16 saboda cin amana
Source: Twitter

"Ta cika fada sosai gashi ba ta da hakuri. Da abu kadan ya hada mu sai ta nemi tayi fada da ni.

"Ba ta rike amanar aure, ba ta iya zama gida ta kula da yara sai dai ta rika fita waje tana bin wasu mazaje kuma idan nayi magana sai tayi barazanar kashe ni.

"Ina rokon wannan kotun mai daraja ta raba mu, babu soyaya ko kauna tsakanin mu kuma babu abinda zai sanya muyi sulhu," kamar yadda ya shaidawa kotu.

Mai shigar da karar kuma ya roki kotu ta bashi damar rike yaransu uku yayin da dan autansu mai shekaru biyar zai cigaba da zama dai mahaifiyar shi amma zai rika ba ta kudin kulawa da shi.

Wanda akayi kara itama ta amince da karar da mijinta ya shigar na raba aurensu amma ta roki kotun ta bawa mijin karamin yaransu ya rike tare da sauran biyu kamar yadda kamfanin dillancin labarai, NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel