Gwamnatin Tarayya na neman hanyoyin bunkasa samun kudin shiga - Udoma

Gwamnatin Tarayya na neman hanyoyin bunkasa samun kudin shiga - Udoma

Gwamnatin tarayya ta fito ta bayyana cewa jama’a su daina dar-dar game da makukun bashin da ke wuyan Najeriya a halin yanzu. Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na Najeriya ya fadi wannan.

Mista Udoma Udo Udoma, yana cewa babu wani dalili na daga hankali a kan bashin da ake bin Najeriya. Ministan tsare-tsaren kasar ya fadi wannan ne bayan taron majalisar zartarwa na FEC na Ranar Laraba 10 ga Watan Afrilu.

Ministan ya tabbatar da cewa Najeriya tana fama da cikas wajen samun kudin shiga amma yayi alkawarin cewa gwamnatin tarayya tana bakin kokarin ta na ganin an shawo kan wannan matsala, nan ba tare da jimawa ba.

Kamar yadda Manema labarai su ka rahoto a tsakiyar makon nan, Minista Udo Udoma yace da zarar Najeriya ta habaka yadda ta ke samun kudin shiga, gwamnatin kasar ba za ta samu wahalar biyan bashin da ake bin ta ba.

KU KARANTA: IMF ta fadawa Buhari ya daina cin bashi daga China

Gwamnatin Tarayya na neman hanyoyin bunkasa samun kudin shiga - Udoma

Gwamnatin Buhari ta arowa Najeriya Naira Tiriliyan 12 a shekaru 3
Source: Depositphotos

Udoma ya fadawa manema labaran da ke fadar shugaban kasa cewa gwamnatin shugaba shugaba Buhari tana bakin kokarin ganin ta kara yawan wadanda ke biyan kudin haraji a Najeriya tare da kuma inganta hanyar karbar kudin.

Bayan nan kuma babban Ministan yace sun bazama wajen ganin hanyar da za a bi na kara samun kudin shiga a gidan kwastam ta hanyar tatso kudi ta kan iyakokin Najeriya. Ministan yace wannan zai taimakawa tattalin Najeriya.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo shi ne ya jagoranci taron FEC da aka yi a makon nan a fadar shugaban kasa tare da Ministocin kasar. A cikin shekaru 3, Shugaba Buhari ya aro bashin kudi na kusan Naira Tiriliyan 11.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel