Kabiru Marafa ya yi ma Saraki tayin kyakkyawar budurwa sakamakon tallafa ma Zamfara

Kabiru Marafa ya yi ma Saraki tayin kyakkyawar budurwa sakamakon tallafa ma Zamfara

Sanata mai wakiltar jama’an mazabar Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa, Kabiru Marafa ya yi ma shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki tayin wata kyakkyawar budurwa domin ta zamno sabuwar amaryarsa sakamakon irin taimakon da yake yi ma jama’an jahar Zamfara.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Marafa ya bayyana haka ne a zaman majalisar na ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu yayin da yake jinjina ma yayan majalisar dattawan, tare da gode musu bisa amincewa da suka yi da ware naira biliyan goma son kulawa da jama’an jahar Zamfara.

KU KARANTA: Kana da labarin Matar da tafi kowacce mace arziki a duk fadin Najeriya?

Sanin kowane cewa matsalar tsaro tayi ma jahar Zamfara katutu, wanda ya danganci hare haren yan bindiga, barayin shanu da kuma masu garkuwa da mutane, wanda hakan yayi sanadiyyar asarar rayukan jama’a da dama, da kuma dimbin dukiya.

Da yake jawabinsa, Sanata Marafa ya bayyana cewa akwai bukatar kara mata a gidan Saraki, saboda a duk lokacin da yaje gidansa, yana fahimtar cewa gidan yayi ma mata daya girma, don haka Saraki na bukatar sabuwar amarya.

“Jama’ana sun nemi na bayyana godiyarsu a gareka sakamakon kokarin da mu duka mukayi a majalisa wajen shawon kan matsalar tsaro a jahar Zamfara. Akwai wata budurwa a mazabata da tace na fada maka cewa bata taba ganin ka buga gudumar majalisa kamar yadda kayi akan amincewa da tallafin jahar Zamfara a jiya ba.

“Don haka tace ta mika kanta gareka don ka aureta idan har kana da bukatar auren, toh amma nace mata ta dakata har sai mun ga alkalumman cikin kasafin kudin shekarar 2019. Toh amma tare da girmamawa ga uwargidarka, ta shirya samun abokiyar zama.” Inji shi.

Daga karshe Marafa ya mika godiyarsa data jama’ansa zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa namijin kokarin da yake yi wajen shawo kan matsalar tsaro a jahar Zamfara, shima Saraki ya gode ma duk yan majalisun da suka tofa albarkacin bakunansu wajen tabbatar da wannan tallafi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel