Ban yi da-na-sani ba inji Zango bayan shigar da shi Kotu

Ban yi da-na-sani ba inji Zango bayan shigar da shi Kotu

- Adam Zango yayi magana a kan rikicin sa da Ali Nuhu

- Yace sam bai yi nadamar fitowa ya kare Mahaifiyarsa ba

- Yanzu haka za a shiga kotu tsakanin manyan Taurarin

Idan ba ku manta ba a yau Ranar Alhamis, 11 ga Watan Afrilun 2019 ne aka shigar da karara babban ‘Dan wasa Adam A Zango a gaban kotu. Ba kowa bane ya kai wannan Tauraro kara face Takwaran sa watau Ali Nuhu.

Bayan Adam Zango ya ji labarin wannan sammaci, ya fito shafin sa na Facebook ya godewa Ubangiji na samun damar wanke kan sa. Kotu dai ta nemi Fitaccen ‘dan wasan ya zo kare kan sa daga tuhumar da ake yi masa.

KU KARANTA: An yi jita-jitar rasuwar wani Dan wasan kwaikwayon Hausa

Ban yi da-na-sani ba inji Zango bayan Ali Nuhu an shigar da shi Kotu

Martanin da Zango yayi bayan ya ji labarin sammacin kotu
Source: Twitter

Babban ‘Dan wasan ya nuna cewa a shirya yake da ya halarci zaman kotun da za ayi inda yake cewa Allah ya nuna masa zuwan wannan rana. Tauraron ya kara da cewa sam bai yi da na sanin fitowa ya kare Mahaifiyarsa ba.

Alhaji Adam Zango a jawabin na sa yake cewa ba zai bari a ci mutuncin Mahaifiyarsa yana ji yana gani ba. Zango a karshen jawabin na sa yake cewa ko me zai faru da shi a dalilin kokarin kare martabar uwarsa, ba zai damu ba.

A cikin ‘yan kwanakin nan ne Adam Zango yake zargin cewa Ali nuhu ya tunzura Yaransa su ci masa mutunci, wannan ya sa shi ma ya fito ya maida a gaban Duniya a kafafen sadarwa na zamani

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel