Ina mafita: Kashi 9 cikin 10 na talaucin duniya zai kare a nahiyar Afirka, a shekarar 2030 - Bankin Duniya

Ina mafita: Kashi 9 cikin 10 na talaucin duniya zai kare a nahiyar Afirka, a shekarar 2030 - Bankin Duniya

- Shugaban babban bankin duniya ya yi wani sharhi, akan irin talaucin da yankin nahiyar Afirka zai shiga nan da shekaru 10 masu zuwa

- Shugaban ya bayyana cewa a cikin kashi goma na matalautan duniya kashi tara za su fito daga nahiyar Afirka ne

- Shugaban ya shawarci shugabannin nahiyar Afirka da na duniya ba ki daya akan su farga da irin matsalar da ta ke tunkaro al'umma

Daga shekarar 1990 zuwa 2000, an samu raguwar talauci da mutane miliyan dari bakwai a duniya. Amma kuma ana samun karuwar mutane da suke zaune cikin matsanancin talauci a yankin nahiyar Afirka.

Shugaban bankin duniya, David Malpass, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake magana da manema labarai a wani taro da ya halarta wanda bankin duniya da bankin IMF suka hada a birnin Washington.

Ina mafita: Kashi 9 cikin 10 na talaucin duniya zai kare a nahiyar Afirka, a shekarar 2030 - Bankin Duniya

Ina mafita: Kashi 9 cikin 10 na talaucin duniya zai kare a nahiyar Afirka, a shekarar 2030 - Bankin Duniya
Source: Depositphotos

A cewar shugaban, a shekarar 2030, kashi 9 cikin 10 na talakawan duniya zasu kasance 'yan yankin nahiyar Afirka ne, sannan kuma rabi na matalautan duniya zasu kasance cikin tashin hankali da rikici.

KU KARANTA: Dangote ya bayyanawa matasa hanyar da za su zama kamar shi

"Wannan sanarwa ce ta gaggawa ga kasashen duniya, musamman na yankin nahiyar Afirka, da ma al'ummar duniya baki daya da su tashi tsaye, domin daukar mataki akan wannan babbar matsalar da ta ke tunkaro mu," in ji shugaban babban bankin duniya David Malpass

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel