Duk masu cin gajiyar N-Power zasu samu albashinsu cikin satinnan - Gwamnati
Babban hadimin shugaban kasa akan harkar samar da ayyuka ga matasa, Afolabi Imoukhuede ya tabbatar ma matasan dake cin gajiyar tsarin daukan aiki na gwamnatin tarayya na N-Power cewa zasu sau albashinsu na watan Maris cikin satin nan.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Afolabi ya bada wannan tabbaci ne a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, yayin da yake musanta zargin da wasu ke yi na danganta nukusanin biyan albashin ga dabarar dakatar da biyan N-Power gaba daya.
KU KARANTA: Gani ga wane: Fusatattun matasa sun kona wani dan fashi kurmus
Gwamnatin shugaba Buhari ne dai ta kikiro tsarin N-Power, inda ta dauki matasa dubu dari biyar aiki, tare da biyan wasu albashin naira dubu talatin, wasu kuma albashin naira dubu goma goma a duk wata, ya danganta da aikin da mutum yake yi.
Yayin da wani kaso daga cikin masu cin gajiyar N-Power suka kasance matasa ne da suka kammala karatun digiri da aka turasu makarantu da Asbitoci don yin aiki, sauran kuma matasa ne masu koyon sana’o’in hannu da gwamnati zata taimaka musu da kayan aiki.
Sai dai rukunin masu cin gajiyar na farko da aka fara dauka ne suka fi nuna zakuwarsu ga rashin biyan albashin na watan Maris, inda suke ganin wata dabarace ta sallamarsu daga tsarin gaba daya, amma hadimin shugaban kasan ya musanta hakan, inda yace har rukuni na biyun ma basu samu albashinsu ba.
A cewar Afolabi, wata matsala ce aka samu a ma’aikatar kudi da ofishin babban akanta na kasa, wanda ta haddasa wannan matsalar, amma tuni an kammala warware wadannan matsaloli, don haka a cikin makonnan duk dan N-Power zai shaki kudinsa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng