Farashin Man Fetur ya yi tashin doron zabuwa a jihar Bayelsa

Farashin Man Fetur ya yi tashin doron zabuwa a jihar Bayelsa

Duk da barazanar cibiyar kula da ma'adanan man fetur ta rufe gidajen mai masu sayarwa sama da farashin gwamnati, ana sayar litar man fetur a kan farashin N155 da kuma N160 a wasu gidajen mai na jihar Bayelsa.

A yayin da cibiyar kula da ma'adanan man fetur DPR ta yi barazanar rufe duk wasu gidajen mai masu sayarwa a kan farashi sama na N145 da gwamnati ta kayyade, ana sayar da man fetur a kan farashin N155 zuwa N160 a jihar Bayelsa.

Farashin Man Fetur ya yi tashin doron zabuwa a jihar Bayelsa
Farashin Man Fetur ya yi tashin doron zabuwa a jihar Bayelsa
Asali: UGC

Da yawa daga cikin gidajen man fetur sun dakatar da harkokin su na cinikayya tun a ranar Juma'a da ya yi sanadiyar karanci da wahalar man fetur tare da haifar da dogayen layuka a gidajen mai na jihar Bayelsa.

Rahotanni kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito sun bayyana cewa, an samu sauki na wahalar man fetur sai dai tsadar farashin sa ya tsananta inda al'umma da dama ke ci gaba da bayyana koken su tun makon da ya shude kawowa yanzu.

Kungiyar 'yan kasuwar man fetur ta IPMAN reshen jihar Bayelsa, ta alakanta tsadar farashin man fetur da tashin farashin sa a wurin masu dillancin sa.

KARANTA KUMA: Za mu tallafa wajen yakar ta'addanci a jihar Zamfara - Gwamna Yari ya shaidawa hukumomin tsaro

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, karamin ministan man fetur Dakta Emmanuel Ibe Kachikwu, a ranar Lahadi ya ce 'yan Najeriya su sha kurumin su tare da kwantar da hankali domin kuwa akwau wadataccen man fetur a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng