Kalli yadda Ministan Buhari ya gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarsa
A ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu ne ministan shari’a, kuma guda daga cikin jigogin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abubakar Malami zai cika shekaru hamsin da biyu a rayuwa, wanda hakan yasa ya shirya kwaryan kwaryan walima.
Legit.ng ta ruwaito an gudanar da wannan bikin murnar cikar Abubakar Malami shekaru 52 ne a gidansa dake babban birnin tarayya Abuja, wanda ya samu halartar gwamnan jahar Kebbi, Atiku Bagudu, da kuma wasu yan uwa da abokan arzikin ministan.
KU KARANTA: Yan bindiga sun halaka mutane 18 tare da barnata dimbin dukiya a Katsina
Uwargidar Malami, Hajiya Fatima ta bayyana maigidanta a matsayin mutumin daya samu tarin nasara a rayuwarsa, kuma shugaba nagari wanda ya bayyana gogewarsa a harkar shugabanci tun bayan darewarsa mukamin minista.
Shi dai Malami an haifeshi ne a ranar 17 ga watan Afrilu na shekarar 1967 a Birnin Kebbi, kuma yayi karatun sharia a jami’ar Usmanu Danfodiyo dake jahar Sakkwato, bayan kammala karatunsa kuma ya fara aiki a kotun majistri a Kebbi.
A shekarar 2003 aka nadashi kwamitin sauraron korafi na zabukan kananan hukumomi a jahar Kebbi, sa’annan ya taba rike mukamin sakataren watsa labaru na kungiyar lauyoyi Musulmai daga shekarar 2002-2004.
Daga bisani Abubakar Malami ya koma jami’ar Usmanu Danfodiyo inda ya koyar a tsangayar ilimin sharia na dan wani lokaci, inda daga nan kuma ya koma ya zama lauya mai cin gashin kansa, a shekarar 2008 ya samu lambar girma ta SAN, a haka har ya zama jami’in shari’a na jam’iyyar CPC ta Baba Buhari.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng