Ambaliyar ruwan sama ta rushe gidaje 48, ta raba mutane 285 da gidajensu a jihar Filato

Ambaliyar ruwan sama ta rushe gidaje 48, ta raba mutane 285 da gidajensu a jihar Filato

Wata mummunar ambaliyar ruwan sama a jihar Filato ta rushe gidaje a kalla 48 tare da raba a kalla mutane 285 da gidajensu a karamar hukumar Mangu.

Lamarin da ya faru a ranar Talata da yamma, ya jefa gwamantin jihar Filato da ta karamar hukumar Mangu cikin damuwa.

Ambaliyar ta fi tsananta a yankin Toghomwol-Bungha da ke karamar hukumar ta Mangu.

Annobar tayi sanadiyyar rushewar gidaje gaba daya ko kuma yin awon gaba da rufin gidajen, lamarin da ya tilasata jama'a barin yankunan da abin ya shafa.

"Ina da yara shida, amma ambaliyar ruwan ta lalata gidanmu gaba daya. Ba ni da wani wuri da zan je na zauna da iyalina yanzu," a cewar Mista Dabit, wani mutum da annobar ta shafa.

Ya ce rashin zabin da ya ke da shi, ya tilasta shi kai iyalinsa gidan 'yan uwa.

Ambaliyar ruwan sama ta rushe gidaje 48, ta raba mutane 285 da gidajensu a jihar Filato

Ambaliyar ruwan sama
Source: Facebook

Dabit ya yi kira ga hukumomi da su kawo masa agaji saboda ya rasa gidansa.

Tuni mataimakin gwamnan jihar Filato, Farfesa Sonni Tyoden, tare da wakilan hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar suka ziyarci karamar hukumar Mangu, inda suka jajanta wa jama'a tare da daukar alkawarin basu tallafi.

DUBA WANNAN: Buhari ya amince da kashe N1.3bn don biyan hakkin ma'aikatan da suka mutu

Tyoden, ya yi kira ga jama'ar yankin Toghomwol-Bungha da su dauki abin da ya faru a matsayin kaddara daga ubangiji.

Mataimakin gwamnan ya bawa wadanda iftila'in ya afka wa tallafin N1m daga aljihunsa.

Kazalika, shugaban karamar hukumar Mangu, Lawrence Danat, ya bayar da tallafin N200,000, yayin da kwamishinan kasuwanci da masana'antu, Mista Usman Idi Bamaiyi, ya bayar da tallafin N50,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel