Yadda wata Mata ta haifi jaririya mai dauke da kai 2 a jahar Sakkwato

Yadda wata Mata ta haifi jaririya mai dauke da kai 2 a jahar Sakkwato

Inda inji Hausawa, ka sha kallo, an samu wata mata mai dauke da juna biyu data haifo wata jaririya, amma ba kamar yadda aka saba ganin jarirai sabbin haihuwa ba, ita wannan jaririyar an haifetane dauke da kawuna guda biyu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a Asibitin Garwa General Hospital dake jahar Sakkwato a ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu, kamar yadda babban likitan Asibitin, Dakta Malami Muhammad Gada ya bayyana.

KU KARANTA: Kifa daya kwala: Yadda dan dambe ya sumar da budurwa tsawon kwanaki 2 da naushi daya

A jawabinsa, Dakta Gada ya bayyana cewa unguwan zomon Asibitin ne suka nemi yazo ya duba wata mata data shigo tana nakudan haihuwa, kuma alamu sun nuna tana fama da doguwar nakuda ne, kuma daga wani kauye ta fito.

Likitan yace da misalin karfe 5 na yamma aka shigo da matar asibiti, kuma sun yi iya bakin kokarinsu wajen ganin ta haihuwa lafiya, amma abin yaci tura, har ma abinda ake sa ran haifa ta rasu a cikin cikin mahaifiyarta sakamakon doguwar nakudan da tayi fama dashi.

“Tunda muka lura jaririyar ta rasu, sai muka yi dabarbaru wajen cirota daga mahaifiyar matar ba tare da munyi mata tiyata ba, saboda jaririyar ta kafa ta fito, kanta na cikin ciki, daga karshe mun samu nasarar zarota, amma sai muka ganta da kai biyu.” Inji shi.

Da ake tambayeshi ko sun taba samun irin wannan a Asibitin, sai Dakta Gada yace basu taba samun haihuwar jaririya mace mai kai biyu a Asibitin ba. Amma likitan yace irin wannan baya rasa nasaba da irin magungunan da masu juna biyu ke sha.

Daga karshe yayi kira ga Mata masu juna biyu dasu dinga zuwa ana musu awo, domin a cewarsa da ace matar nan tana zuwa awo Asibiti, toh da anyi hoto an gane halin da jaririyarta ke ciki, kuma da an haifi jaririyar da ranta cikin sauki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: