An bayyana masu zartar da ta'addanci a jihar Zamfara

An bayyana masu zartar da ta'addanci a jihar Zamfara

Kungiyar masu hako ma'adanan kasa ta Najeriya, a ranar Talata ta bayyana cewa, 'yan baranda da kuma miyagun masu hako ma'adanai na makotan kasashe da su ka hadar da Burkina Faso, Chad, Nijar da kuma Ghana ke da alhakin haifar da ta'addanci a jihar Zamfara.

Kungiyar ta ce ire-iren baragurbin masu hako ma'adanan kasa da su ka ketaro daga kasashen Burkina Faso, Chadi, Nijar da kuma Ghana dauke da miyagun makamakai ke da alhakin kashe-kashen da sauran miyagun ababe da ke aukuwa a jihar Zamfara.

Jihar Zamfara

Jihar Zamfara
Source: Facebook

Shugaban kungiyar, Kabiru Kankara, shi ne ya bayyana damuwar sa a kan kashe-kashe da zubar jinin al'umma da ke ci gaba da aukuwa a jihar Zamfara. Ya yi babatun yadda gwamnatin tarayya ta yi jinkiri wajen haramta hako ma'adanan kasa a jihar.

Kankara ya ce gabanin hukuncin da gwamnatin tarayya ta zartar, tun a baya sahihan kungiyoyi masu hako ma'adanai sun yi kira na neman a kawo masu daukin a akan yadda 'yan baranda da kuma miyagun masu hako ma'adanai su ka zamto alakakai a gare su.

A yunkurin gwamnatin tarayya na kawo karshen ta'addanci da ya zamto ruwan dare a jihar Zamfara, a ranar Lahadi 7 ga watan Afrilu, ta bayar da umurnin haramta duk wasu harkokin na hako ma'adanan kasa jihar da kewayen ta.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na sauka daga kujera ta a 2015 - Jonathan

Sufeto Janar na 'yan sanda, Muhammad Adamu, shi ne ya bayar da wannan sanarwa yayin ganawar sa da manema labarai a lokacin ziyarar gani da idanu da daura damarar tunkurar zulumin da al'ummar jihar Zamfara ke fuskanta.

Kazalika sufeton na 'yan sanda ya jaddada tsayuwar daka ta shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen kawo karshen annoba ta rashin tsaro da ta yi kane-kane a wasu sassan kasar nan musamman jihar Zamfara da Kaduna.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel