Sai an tsige Magu kafin 29 ga watan Mayu - Wasu gwamnoni na Sanataco na shirya tuggu

Sai an tsige Magu kafin 29 ga watan Mayu - Wasu gwamnoni na Sanataco na shirya tuggu

Sai an tsige Magu kafin 29 ga watan Mayu

Yayin da sabon wa’adin mulki ke gabatowa inda za’a tsantar da sabbin gwamnoni da kuma yan majalisar dattijai wasu daga cikinsu na bada matsi akan cewa lallai a tsige Mallam Ibrahim Magu a matsiyinshi na shugaban rikon kwaryar hukumar EFCC.

Labari daga Legit.ng na cewa suna tsananin matsa lamba ga fadar Shugaban kasa don ganin cewa anyi waje da Magu daga wannan mukami nasa.

Majalisar dattijai

Majalisar dattijai
Source: Depositphotos

KU KARNATA:Kotun daukaka kara ta soke zaben zababben sanatan APC Sani Musa

Wata majiya ta fahimci Gwamnoni basu gamsu da binciken da Magu yayi ba akan Shugaban Alkalai mai murabus, Walter Onnoghen.

Wannan shine karo a uku cikin shekara biyu da akayi yunkurin tsige Magu da mukaminsa daga yan siyasa ta basu goyon bayan yaki da cin hancin da Gwamnati Buhari keyi.

Akwai shirin tura Magu domin karo karatu a National Insitute for Policy and Strategic Studies (NIPSS) kafin ko kuma bayan zabe.

Zance dake nan a yanzu shine na a tsige Magu kafin ko kuma ranar 29 ga watan Mayu a dai dai lokacin da wasu daga cikin Gwamnonin suk cika shekara takwas na mulkinsu.

Wata majiya mai tushe, ta shaidama wakilinmu cewa wadanda ke son ganin an raba Magu da kujerar sun bayyana cewa barin Magu ka iya zama barazana ga kudurin jam’iyar APC a 2023.

Majiyar ta kara da cewa: “Masu hura wannan wutar na yin hakan ne don bata Magu a idanun Buhari, Osinbajo da Aisha Buhari.

Sun fake ne akan wani rahoto na bugi akan Magu da aka aikewa Fadar Shugaban kasa ta hanyar wata ma,aikata gwamnati da ba’a santa ba.

Sun kara da cewa Magu mutum ne wanda bai da amana domin yana sabawa jam’iyar APC daga yanzu har izuwa 2023.

Sun kuma yi nuni zuwa ga yadda hukumar EFCC tayi sanadiyar ajiye aiki da Onnoghen yayi na kwatsam. Hakan yasa suke ganin Magu zai iya yin komai ganin cewa ya tona duk wani aisiri nasu musamman lokacin da suke bari ofis.

Har wayau suna zargin cewa tunda ba a rasa wata yar matsala ba tare dasu Magu zai iya amfanin da wannan damar tasa ya gabatar dasu a gaban shari’a.

Wadanda ke zuzuta wanna kuduri na daga cikin wasu yan jam’iyar APC da PDP.”

Labari yazo cewa wasu senatoci sunyi gangami domin ganin yadda Magu yake fada da cin hanci da rashawa.

Wannan majiyar ta kara da cewa: “Wasu senatoci sam basu goyon bayan tabbatar da Magu a matsayin Shugaban hukumar ta EFCC domin yin hakan tamkar barazanace a garesu saboda zai iya bibiyarsu da zarar wa’adin mulkinsu ya kamala.

Suna sane da binciken da akeyi akansu wanda ya hada da naira tiriliyan daya na ayyuka gundumomi, lallai sun sani cewa Magu ba zai aminta da wannan ba sam.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel