Michael Jordan shi ne ‘Dan wasan da ya fi arziki a 2019 - Forbes

Michael Jordan shi ne ‘Dan wasan da ya fi arziki a 2019 - Forbes

Jama’a da da-dama su na tambaya a game da wanene ‘dan wasan da ya fi kowa dukiya a Duniya. Wannan ya sa mu kayi bincike mu ka kawo maku ‘dan wasan da ya fi arziki kamar yadda Mujallar Forbes ta Duniya ta bayyana.

Kamar yadda Forbes ta nuna, Michael Jordan shi ne wanda ya fi kowa kudi a cikin masu wasannin motsan jiki. A lokacin da Jordan yake wasa, ya tara makudan kudi da su ka haura fam Dala Miliyan 90 a matsayin albashin sa.

Bayan wadannan kudi da Michael Jordan ya samu wajen buga wasan kwando, mafi yawan dukiyar sa ba sun fito bane daga harkar buga wasan Kwando. Micheal Jordan yayi arziki ne wajen yi wa manyan kamfanonin Duniya talla.

KU KARANTA: Za a bayyana sabon Kocin Kungiyar Man Utd

Michael Jordan shi ne ‘Dan wasan da ya fi arziki a 2019 - Forbes

Tsohon 'Dan wasan kwando Michael Jordan yana cikin Attajiran Duniya
Source: Facebook

Jordan ya bugawa kungiyar Chicago Bulls da Washington Wizards ne a lokacin yana wasa a cikin shekarun 1980 zuwa 1990. Kusan dai da wuya a samu wanda ya zarcewa Jordan a tarihin wadanda su ka buga wasan kwando a Duniya.

‘Dan wasa Jordan ya samu sama da Dala Biliyan 1.4 a sanadiyyar aiki da wasu kamfanoni. Forbes ta rahoto cewa a cikin farkon shekarar nan ta 2019, tsohon ‘dan wasan kwandon yana da fiye da Dala Biliyan 1.7 a asusun bankin sa.

A cikin tsofaffin ‘yan wasan da su kayi ritaya da kuma masu buga wasa a yanzu, babu wanda ya kama kafar Jordan a fuskar Duniya. Jordan shi ne na 1447 a cikin sahun masu kudin Duniya gaba daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel