Farfesa Mohammed: Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ta samu sabon shugaba
Majalisar gudanarwa ta jami’ar gwamnatin tarayya ta tunawa da tsohon Firai ministan Najeriya, Abubakar Tafawa Balewa dake jahar Bauchi, watau Abubakar Tafawa Balewa University, ATBU, ta sanar da nadin sabon shugaban jami’ar.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito majalisar ta sanar da sunan Farfesa Mohammed Abdulazeez a matsayin sabon shugaban jami’ar, watau Vice Chancellor, kamar yadda sakataren majalisar, Ahmed Hassan ya sanar a garin Bauchi a ranar Asabar.
KU KARANTA: Bankin Musulunci ta Duniya ta baiwa Najeriya tallafin N186,000,000 domin aikin Hajji
Sakataren majalisar ya bayyana cewa majalisar ta tabbatar da Mohammed a matsayin sabon shugaban jami’ar ne a yayin zamanta na musamman karo na 26 bayan samun amincewar kungiyoyin jami’ar da kuma amincewa majalisar koli ta jami’ar.
Haka zalika sanarwar daga bakin sakataren ta kara da cewa Farfesa Mohammed Abdulazeez ya doke mutane biyu wadanda suka sha gwagwarmaya tare da fafatawa wajen neman wannan muhimmin kujera a jami’ar.
Sanarwar bata karkare ba sai da ta bayyana cewa sabon shugaban jami’ar zai yi wa’adin mulki daya ne na tsawon shekaru biyar, faraway daga ranar 26 ga watan Afrilun shekarar 2019, kamar yadda dokar jami’o’I ta shekarar 2003 ta tanadar.
Sai dai dama can an dade ana bugawa da Mohammed a sha’anin mulki a jami’ar, inda kafin wannan nadi nasa shine mataimakin shugaban jami’ar mai kula da sha’anin tafiyar da mulki, kuma Farfesa ne a bangaren ilimin Physics.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng