Kakakin Majalisa Dogara zai nemi ya nada na-kusa da shi a kujerar sa

Kakakin Majalisa Dogara zai nemi ya nada na-kusa da shi a kujerar sa

Rahotanni na zuwa mana cewa, a halin yanzu akwai ‘yan majalisa rututu da su ke neman kujerar shugaban majalisar wakilan tarayya wanda Rt. Hon. Yakubu Dogara yake shirin bari bayan ya koma PDP.

Daily Trust ta bayyana cewa wadanda su ka kwallafa rai a kan kujerar Yakubu Dogara sun hada da irin su Honarabul Ahmed Idris Wase, Umar Mohammed Bago, Abdulrazak Namdas, Babangida Ibrahim da kuma Muktar Aliyu Betara.

Jaridar tace haka zalika Honarabul John Dyegh na Benuwai yana cikin masu harin wannan kujera. A tarihin siyasar Najeriya tun 1999, Yankin Arewa maso tsakiya ba su taba kawo shugaban majalisar wakilai ko mataimakin sa ba.

KU KARANTA: Babu mamaki a sake maimaita abin da ya faru 2015 a 2019 a Majalisa

Yanzu haka dai nan ne inda John Dyegh, Ahmed Idris Wase da kuma Umar Mohammed Bago su ka fito. Honarabul Umar Mohammed Bago yana cikin manyan na-hannun daman Yakubu Dogara da ake tunani za a gwabza da shi a bana.

Ita dai jam’iyyar APC mai rinjaye a majalisa ta bayyana cewa Honarabul Femi Gbajabiamila ta ke so ya gaji Yakubu Dogara a majalisa ta 9. Akwai yiwuwar a gama Hon. Gbajabiamila tare da Ahmed Wase a matsayin mataimakin sa.

Da alamu Mutanen da ke tare da Yakubu Dogara, wanda ke rike da wannan mukami a halin yanzu ba su tare da Femi Gbajabiamila. Wannan ya sa su ka fara aiki a kasa na ganin cewa wanda su ke so ne ya samu wannan kujera a zaben.

KU KARANTA: Manyan abubuwa 8 da su ka faru a zaben Jihohin Najeriya

Daga cikin wadanda ake gani sun fi kusa da Yakubu Dogara a majalisar akwai Umar Bago, Babangida Ibrahim, Abdulaziz Namdas da kuma Mukhtar Betara. Ba a dai san wanene Dogara zai marawa baya daga cikin wadannan ba.

Irin su Namdas, Babangida da kuma Betara za su samu matsala saboda yankin da su ka fito daga Arewacin kasar. Shi kuma Dyegh wanda a da yake goyon bayan Wase, ya balle daga tafiyar inda ya nuna cewa zai fito takara da kan sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel