Osinbajo ya shilla zai halarci taro a kasar Rwanda

Osinbajo ya shilla zai halarci taro a kasar Rwanda

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya fice daga Najeriya domin halartar taron tunawa da gagarumar kisan gillar da ta auku kan 'yan kabilar Tutsi a kasar Ruwanda shekaru 25 da suka gabata.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Farfesa Osinbajo tare da sauran shugabannin kasashen duniya da kuma manyan baki, za su halarci taron da za a gudanar da a ranar Lahadi, 7 ga watan Afrilun 2019 cikin babban birnin kasar Rwanda watau Kigali.

Osinbajo

Osinbajo
Source: Facebook

Mai magana da yawun Mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, shi ne ya bayar da shaidar hakan tare da bayyana yadda taron zai gudana daki-daki bisa jagorancin mai masaukin baki, shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame.

Tarihi ba zai mance da yadda 'yan asalin kasar Rwanda bisa jagorancin gwamnati da ake masu lakabi da kabilar Hutu, su ka yiwa bakin haure da ake kira kabilar Tutsi, diban karan Mahaukaciya na kisan kiyashi a ranar 7 ga watan Afrilun 1994.

KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta yi alhinin mutuwar tsohuwar shugabar hukumar NAFDAC, Dora Akunyili

An shafe tsawon watanni uku ana tafka bakin gumurzu yayin da adadin rayukan da suka salwanta ya kai kimanin 500,000 zuwa 1,000,000. Majalisar dinkin duniya ta taka rawar gani wajen assasa tunawa da wannan mummunar rana ta bakin ciki a shekarar 2003.

A yayin da ake sa ran dawowar mataimakin shugaban kasa a Yammacin yau na Lahadi, maruwaita tarihi sun yi itifakin cewa kasar Rwanda ta tsamo kanta daga cikin kangin durkushewa sakamakon jajircewa ta shugaban kasa Kagame.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel