Na yafe wa mutumin da ya kashe mini 'ya'yana

Na yafe wa mutumin da ya kashe mini 'ya'yana

Yanzu shekaru 25 kenan bayan yakin basasa a kasar Rwanda, inda aka dinga yi wa mutane kisan kiyashi

Wata mata mai suna Anne-Marie ta na daya daga cikin mutanen da abin ya rutsa da su, inda wani mutumi ya fille wa 'ya'yanta guda biyu kai akan idonta.

Anne-Marie ta sha dakyar daga kisan kare dangin kasar Rwanda wanda aka yi a shekarar 1994. Sai dai kuma babban danta mai suna Anne-Marie Uwimana dan shekaru 11 bai tsallake yakin ba.

In ji matar ta ce: "Ya yi alkawarin kula da ni tare da inganta rayuwata. Yana da kirki matuka."

Na yafe wa mutumin da ya kashe mini 'ya'yana

Na yafe wa mutumin da ya kashe mini 'ya'yana
Source: Facebook

A watan Afrilun 1994 makwabcinta Celestin ya kai mata hari.

"A gabana Celestin ya zaro makami ya fille wuyan 'ya'yana biyu, ni kuma na gudu don na tsira da raina."

Matar ta shira, amma kuma ta rasa komai nata. A cikin kwanaki kusan 100 fiye da 'yan kabilar Tutsi da Hutu 800,000 aka kashe.

Wani tsohon dan jarida a kasar mai suna T.Ndahiro ya ce farfagandar gwamnati ce ta kara ta'azzara lamarin. Gidan rediyo da talabijin masu zaman kansu na Libre de Mile Collines sun taimaka sosai.

KU KARANTA: Hanyoyi guda 6 da za a bi don samawa kai sassaucin zafi a wannan lokaci

In ji dan jaridar ya ce: "Su kan kira su da kyankyasai ko macizai, sukan kira su da sunaye iri-iri. Ana kuma yi wa 'yan kabilar Tutsi da lakabi da makiya, makiyan kasar Rwanda."

Bayan kisan kare-dangin, makwabcin Anne-Marie ya koma kauyen na su. Matar ta ce ta so daukar fansa, amma wani Malamin Cocin Catholic ya lallasheta ta yafe masa.

Mutumin mai suna Celestin Habinshuti, ya ce: "Muna neman afuwa daga duk wadanda aka musgunawa. Mun kubuta duk kuwa da ta'asar da muka aikata da kashe mutane da muka yi. Sannan Anne-Marie ta tsira daga harin nawa, Allah ne kuma ya tseratar da ita."

Celestin ya shekara 10 a gidan yari kuma har zuwa yanzu yana neman afuwa. Duk da cewa raunukan yakin sun warke, amma har yanzu radadin shi yana nan a cikin zukatan mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel