Buhari na kan cika ma yan Najeriya alkawarin daya daukan musu – fadar shugaban kasa

Buhari na kan cika ma yan Najeriya alkawarin daya daukan musu – fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika ma yan Najeriya duk alkawurran daya daukan musu a yayin yakin neman zabe, musamman da yace ba za’a saki sha’anin sakaka don yakin neman zabe ba.

Haka zalika majiyar Legit.ng ta ruwaito fadar shugaban kasan ta kara da jaddada burin shugaba Buhari na cika ma ma’aikatan Najeriya alkawarin daya dauka na tabbatar da sabon karancin albashi, kuma a yanzu haka ya cika wannan alkawari.

KU KARANTA: Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Miji ya yi ma matarsa yankan rago a Kano, ya binne gawar

Kaakakin shugaban kasa, Femi Adesina ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, a babban birnin tarayya Abuja, inda yace wadannan alkawura da Buhari ya cika ma yan Najeriya ba karamar nasara bace gareshi da gwamnatinsa gaba daya.

“Wasu daga cikin nasarorin da Buhari ya samu yayin da ake gudanar da yakin neman zabe sun hada da batun karancin albashi, samar da kudaden gudanar da manyan ayyukan more rayuwa, da kuma kare hakkin masu sayan kaya.” Inji shi.

Adesina ya bayyana cigaban da aka samu tun bayan rattafa hannu kan dokar gina hanyoyi da yayi a ranar 25 ga watan Janairu, wanda hakan ya baiwa kamfanoni damar gina hanyoyi, sa’annan gwamnati zata rage musu harajin da suke biya.

Inda a yanzu haka yace wasu kamfanoni masu zaman kansu guda shida sun dauki gabaran gina manyan hanyoyi guda goma sha tara (19) a jahohi goma sha daya (11) cikin yankuna shida na Najeriya.

Kamfanonin sun hada da Dangote Industries Limited; Lafarge Africa Plc; Unilever Nigeria Plc; Flour Mills of Nigeria Plc; Nigeria LNG Limited; da China Road and Bridge Corporation Nigeria Limited.

Wasu daga cikin hanyoyin kuma sun hada da titin Ashaka zuwa Bajoga a Gombe, Dikwa zuwa Gambaru-Ngala a Borno, Bama zuwa Banki a Borno, titin Sharada a Kano, titin Nnamdi Azikiwe a Kaduna, titin Birnin Gwari a Kaduna da Birnin Gwari zuwa Dansadau a Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel